Labari mai dadi: An samar da rigakafin Coronavirus a Birtaniya, za'a fara gwadawa jikin marasa lafiya ranar Alhamis

Labari mai dadi: An samar da rigakafin Coronavirus a Birtaniya, za'a fara gwadawa jikin marasa lafiya ranar Alhamis

- Masana ilmin kwayoyin cuta a jami'ar Oxford sun kirkiri rigakafin cutar Coronavirs da ta addabi duniya

- Za'a fara gwajin rigakafin kan mutane ranar Alhamis mai zuwa

- Wannan ya biyo bayan wanda kasar Sin ta samar kuma ta fara gwaji amma har yanzu basu bayyana sakamakon ba

Sakataran kiwon lafiya kasar Birtaniya, Matt Hancock, ya bayyana cewa an samar da rigakafin cutar COVID-19 kuma ranar Alhamis za'a fara gwadawa kan masu cutar.

Masana ilmin Kimiyan jami'ar Oxford ne suka kirkiri rigakafin mai suna ''ChAdOx1 nCoV-19"

Yayinda yake jawabi a taron da aka shirya a fadar shugaban kasar Ingila, 10 Downing Street, Hancock ya ce gwamnatin na iyakan kokarinta wajen samar da rigakafin cutar COVID-19.

Ya ce gwamnatin ta baiwa masana ilmin Kimiyan jami'ar Oxford Yuro milyan 20 (N.9.5bn) domin taimakawa wajen gwajin rigakafin.

Hancock ya ce za'a kara baiwa wasu masana kimiyan na jami'ar Imperial College dake Landan £22.5 million domin nasu binciken.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An sallami mutane 9 daga asibiti bayan warkewa daga Coronavirus

Labari mai dadi: An samar da rigakafin Coronavirus a Birtaniya, za'a fara gwadawa jikin marasa lafiya ranar Alhamis

Rigakafi
Source: UGC

Yace gwamnatin "za ta basu dukkan goyon bayan da suke bukata da kudi har su cimma burin samun nasara cikin kankanin lokaci."

"Kuma daga karshe, hanya mafi inganci na kawar da cutar Korona itace samar da rigakafi. Wannan sabuwar cuta ce, bamu san yadda za'a kare ba, amma ina da tabbacin za muyi iyakan kokarinmu wajen samar da rigakafin."

"Kasar Ingila ce ke kan gaba wajen neman rigakafin a duniya. Mun fi kowace kasa a duniya zuba kudi wajen binciken nemo rigakafi."

"Kuma duk da kokarin da sauran kasashen duniya ke yi, biyun da ke kan gaba a nan suke, Oxford da Imperial."

"Bisa da dukkan kokarin nan da muke yi, ina mai sanar muku da cewa za'a fara gwajin rigakafin da aka kirmiro a jami'arr Oxford ranar Alhamis."

"Gaskiya samun irin wannan nasara kan dauki shekaru amma ina alfahari da aikin da sukayi."

"Ba tare da bata lokaci ba, zamu zuba kudi domin kara samar da rigakafin da yawa idan an samu nasara tayi aiki."

Amma ya bayyana cewa har yanzu babu tabbas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel