Jana’izar Abba Kyari: Jam’iyyar PDP ta nemi a kama sakataren gwamnatin Najeriya

Jana’izar Abba Kyari: Jam’iyyar PDP ta nemi a kama sakataren gwamnatin Najeriya

PDP ta yi kira da a kama sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da sauran wadanda suka halarci jana’izar Abba Kyari tare da gurfanar dasu saboda karya dokar yaduwar COVID-19.

Daily Nigerian ta ruwaito Boss Mustapha, wanda shi ne shugaban kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar COVID-19 a Najeriya, ya halarci jana’izar Abba Kyari a ranar asabar a Abuja.

KU KARANTA: Mutuwa riga: Jami’in tsaron da marigayi Yar’adua ya baiwa Buhari ya rasu

Sai dai Mustapha tare da sauran manyan jami’an gwamnati da suka halarci jana’izar sun karya ka’idojin da gwamnati ta shimfida na yaki da cutar Coronavirus.

Amma bayan gane kuren su, a madadinsu gaba daya, Boss Mustapha ya nemi afuwan gwamnatin Najeriya da jama’an kasar bisa wannan doka da suka keta.

Jana’izar Abba Kyari: Jam’iyyar PDP ta nemi a kama sakataren gwamnatin Najeriya
Jana’izar Abba Kyari
Asali: Facebook

Sai dai kakaakin PDP, Kola Ologbondiyan ya ce jam’iyyarsu bata amince da gafarar da Boss Mustapha ya nema ba, inda yace kamata yayi a kama shi tare da sauran jami’an gwamnatin.

“Jam’iyyarmu ta fahimci sun nemi afuwan ne bayan yan Najeriya sun yi musu ca tare da Allah wadai da yadda suka gudanar da kansu a makabartar da aka binne mamacin.

"PDP na kallon wannan a matsayin abin kunya musamman yadda aka kama mai dokar barci ya bige da gyangyadi.

“Wannan laifi da suka yi ya lalata duk wani kokari da ake yi na yaki da yaduwar annobar a Najeriya, mun dauka manyan jami’an gwamnatin za su karrama Abba Kyari da dabi’un da yan Najeriya za su yi koyi dasu musamman a wannan lokaci ya yaki da COVID-19.

“Wannan ba maganan neman afuwa ko gafara bane, don haka PDP ke kiya ga hukumar babban birnin tarayya ta ta kamasu tare da gurfanar dasu gaban kotu kamar yadda take hukunta yan Najeriya, ba tare da nuna wani bambanci ba.” Inji shi.

Kola ya ce yan Najeriya na ganin yadda hukumar Abuja ke gurfanar da mutane da dama a kotunan tafi da gidanka saboda sun karya dokar ta baci ba tare da la’akari da uzurinsu ba.

Don haka yace idan da adacli wannan shi ne abin da ya kamata gwamnatin ta yi ma sakataren gwamati Boss Mustapha da sauran manyan jami’an gwamnatin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel