Mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da mace mai ciki da yaronta a jahar Yobe
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai samame kauyen Buni Gari a jahar Yobe inda suka kashe wani matashi dan sa kai, suka tafi da wata mata mai dauke da juna biyu da yaron ta.
Daily Trust ta ruwaito yan ta’addan sun far ma kauyen ne dake cikin karamar hukumar Gujba inda suka kaddamar da harin mai kan uwa da wabi, har ma suka jikkata wani mazaunin garin.
KU KARANTA: Jami’an Yansanda sun kama kasurgumin Dan fashi a matattarar yan wiwi

Asali: Twitter
Shaidun gani da ido sun bayyana sunan matashin da yan ta’addan suka kashe a matsayin Kaukau Gada, kuma sun tsince shi ne a wajen garin kwance cikin jini washegarin harin.
Sun kara da cewa yan ta’addan sun banka wuta a wani sashi na makarantar firamarin kauyen da wani gida mallakin wani mutumi dake gudun hijira sakamakon hare haren Boko Haram.
Yan ta’adda sun kai harin ne da misalin karfe 5:10 na yamma a cikin motocin Hilux guda 14, sai dai matasa yan sa kai sun yi artabu dasu, amma suka tsere bayan yan ta’addan sun ci karfinsu.
Ana cikin haka sai dakarun rundunar Sojjin Najeriya suka musu kawanya a kasa, yayin da jiragen yaki suka dinga musu ruwan bamabamai, wanda hakan yayi sanadiyyar karkashe su.
A jawabin rundunar Sojan kasa, ta bayyana cewa ta kashe akalla yan ta’adda 105 a wannan hari, kamar yadda kwamandan shiyya ta 2, Birgediya Lawrence Araba ya bayyana.
Araba ya ce: “Biyo bayan harin da Sojojin shiyya ta 2 na Operation Lafiya Dole suka kai, rundunar Sojin ta tabbatar da kashe yan Boko Haram 105 a artabun da muka yi da su a Buni Gari.
“Mun samu wannan nasara ne sakamakon rahotannin sirri da muka samu wanda ya fallasa shirin da yan ta’addan suke yi na kai ma garin hari.” Inji shi.
Daga karshe Araba ya ce sun kwato bindigu 11, rediyon sadarwa da kuma wata mota mai jigida guda 1.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng