Boko Haram: Shekau ya shirya mika wuya - Rundunar sojin Najeriya

Boko Haram: Shekau ya shirya mika wuya - Rundunar sojin Najeriya

Majiyoyi daga rundunar sojin Najeriya a jiya ta tabbatar da cewa, sakamakon hari babu sassautawa da rundunar ke kaiwa mayakan ta'addanci na Boko Haram da ISWAP, shugaban kungiyar 'yan ta'addan ya shirya mika wuya.

Rundunar ta tabbatar da halaka manyan kwamandojin Boko Haram din a harin da ta kai Durbarda da ke jihar Borno, jaridar ThisDay ta ruwaito.

A yayin bayani daga shugaban yada labarai na rundunar a Abuja, Manjo Janar John Enenche, ya ce manyan alamu sun bayyana karaya da kokarin mika kai da Shekau ke yi ga rundunar.

Ya kara da cewa tuni suka murkushe Boko Haram din sakamakon luguden ruwan wutar da suke musu.

Hakazalika, sun tarwatsa duk wani sansanin 'yan ta'addan da suka sani.

"Idan aka yi maganar alamu, toh babu shakka ya nuna duk wasu alamomi da ke bayyana karaya. Tun bayan da rundunar sojin Najeriya ta saka su a gaba, sun rasa maboya", yace.

Ya kara da cewa, luguden ruwan wutar da rundunar Operation Lafiya Dole ke yi wa 'yan ta'addan ta sama ya jawo ajalin manyan kwamandojin Boko Haram din.

Boko Haram: Shekau ya shirya mika kansa - Rundunar sojin Najeriya
Boko Haram: Shekau ya shirya mika kansa - Rundunar sojin Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Kano bayan mutum 150 sun rasu a cikin kwana 2

"Da yawa daga cikin shugabannin 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP din sun rasa rayukansu. Sansaninsu duk sun tarwatse sakamakon ruwan wuta ta sama da rundunar Operation Lafiya Dole ta yi musu a Durbarda da ke Borno.

"Wannan harin da rundunar sojin ta kaiwa 'yan ta'addan ya biyo bayan bayanan sirrin da suka bayyana inda 'yan ta'addan suka yi sansani," yace.

Ya yi bayani cewa jiragen yakin sojin saman Najeriya sun dinga samun sa'ar sakin ruwan wuta ta dai-dai inda ake bukata, wanda hakan ya jawo mutuwar 'yan ta'adda masu tarin yawa.

"Sauran da aka gano suna yunkurin tserewa kuwa an hanzarta tare su ta kasa.

"Rundunar sojin Najeriya ba za ta yi kasa a guiwa ba har sai ta tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da tsaro mai dorewa a yankin Arewa maso gabas na kasar nan," yace.

A bangare guda, Hedkwatar tsaro ta kasa ta kara da cewa, ta samar da ruwan ”sanitiza” da na'urorin taimakon numfashi don tallafawa gwamnatin Najeriya wajen yakar annobar Covid-19.

Ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohin kasar nan da su dinga amfani da kayayyakin kamfanin hukumar tsaron don karfafa mata guiwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel