Annobar Coronavirus: Najeriya za ta fara kwaso yan kasar waje daga mako mai zuwa

Annobar Coronavirus: Najeriya za ta fara kwaso yan kasar waje daga mako mai zuwa

Gwamnatin Najeriya za ta fara dawo da yan Najeriya da annobar Coronavirus ta rutsa da su a kasashen waje daga mako mai zuwa.

Punch ta ruwaito an samu kamfanonin jiragen sama guda 2 da suka amince su dauko mutanen a kan kudi mai rangwame, kamar yadda ministan harkokin kasashen waje ya bayyana.

KU KARANTA: Kisan mutane 47 a Katsina: Buhari ya yi alkawarin ramuwar gayya a kan yan bindiga

Minista Geoffrey Onyeama ya bayyana haka ne yayin da taron kwamitin shugaban kasa dake yaki da COVID-19 a ranar Litinin, inda yace za’a debo yan Najeriyan ne mutum 200 a duk sawu.

Fiye da yan Najeriya 2,000 a kasar Amurka, Birtaniya, Dubai, China da sauran kasashe ne suka yi rajistan dawowa gida Najeriya bayan sun amince da sharuddan da gwamnati ta gindaya musu.

Annobar Coronavirus: Najeriya za ta fara kwaso yan kasar waje daga mako mai zuwa

Annobar Coronavirus: Najeriya za ta fara kwaso yan kasar waje daga mako mai zuwa
Source: Depositphotos

Daga cikin sharuddan zasu biya kudin jigilarsu, kuma za’a gudanar da gwajin cutar Coronavirus a kan su, sa’annan a killace su tsawon kwanaki 14 da zarar sun sauka a Abuja ko Legas.

Ministan ya ce gwamnati tana kokarin samar da isassun wuraren da za ta killace su, amma yace sun samu kalubale game da gadajen, don haka zasu dinga dauko mutane 200 a sawu.

“Saboda karancin wurin killacesu, shi yasa zamu kwaso mutane 200 a kowanne sawu a Abuja da Legas, idan aka kammala killace su bayan kwanaki 14 sai mu sake kwaso wasu mutane 200.” Inji shi.

A hannu guda, gwamnatin jahar Borno ta samu nasarar binciko mutane 99 da suka yi mu’amala da mutum na farko da ya kamu da annobar Coronavirus mai toshe numfashi a jahar.

Wani jami’in kiwon lafiya ne ya fara kamuwa da cutar a jahar Borno, wanda kuma ta yi sanadiyyar mutuwarsa a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

Wannan jami’in kiwon lafiya yana aiki ne da kungiyar likitoci mai zaman kanta, watau Doctors without borders a kauyen Pulka cikin karamar hukumar Gwoza, inda ya rasu a ranar Asabar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel