Abubuwa 8 da ba dole ka sani ba game da marigayi Abba Kyari

Abubuwa 8 da ba dole ka sani ba game da marigayi Abba Kyari

- Mutuwar Abba Kyari ta jawo cece-kuce daga ‘yan Najeriya. Kafin rasuwarsa, Abba Kyari ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari

- A ranar 23 ga watan Maris, an tabbatar da cewa Abba Kyari ya kamu da cutar coronavirus bayan dawowarsa daga kasar Jamus

- A ranar 29 ga watan Maris, Kyari ya fitar da takarda mai bayyana cewa ya koma jihar Legas don ci gaba da jinya

Mutuwar Abba Kyari ta jawo cece-kuce daga ‘yan Najeriya. Kafin rasuwarsa, Abba Kyari ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A ranar 23 ga watan Maris, an tabbatar da cewa Abba Kyari ya kamu da cutar coronavirus bayan dawowarsa daga kasar Jamus.

A ranar 29 ga watan Maris, Kyari ya fitar da takarda mai bayyana cewa ya koma jihar Legas don ci gaba da jinya.

Bayan kwanaki 21 da fitar wannan takardar ne aka bayyana mutuwar Abba Kyari.

Kafin rasuwarsa, Abba Kyari na daga cikin masu fada a ji a mulkin shugaba Buhari.

Ga wadansu abubuwa da baka sani ba game da marigayi Abba Kyari:

1. Abba Kyari dan asalin kabilar Kanuri ne daga jihar Borno.

2. Kyari ya kammala digirinsa na farko a fannin sanin halayyar dan Adama daga jami’ar Warwick. Ya yi digiri a fannin shari’a a jami’ar Cambridge da ke London.

3. A 1983, ya zama cikakken lauya bayan ya samu horarwa a makaranta lauyoyi ta Najeriya.

Abubuwa 8 da ba dole ka sani ba game da marigayi Abba Kyari
Abubuwa 8 da ba dole ka sani ba game da marigayi Abba Kyari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Ganduje ya sallami kwamishinansa da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari

4. Kyari ya aura sirikar Ibrahim Tahir kuma suna da yara hudu. Ibrahim Tahir ne tsohon ministan harkokin cikin gida. Ya rasu ne a shekarar 2009.

5. Daga 1990 zuwa 1995, Kyari ya zama sakataren African International Bank Limited.

6. Kyari ya zama daraktan gudanarwa na bankin UBA inda daga baya ya zama shugaban bankin. A 2002, an nada shi a matsayin darkatan Unilever Nigeria inda daga baya ya koma Exxon Mobil Nigeria.

7. A watan Augusta 2015, Kyari ya zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari

8. Ya zama dan kwamitin bada shawara a kan hannayen jari a Najeriya tsakanin 2000 zuwa 2005.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel