Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta tayar da komadar wani katafaren jirgin yaki

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta tayar da komadar wani katafaren jirgin yaki

Rundunar Sojan sama ta Najeriya ta samu nasarar gyara wani jirgin yakin Najeriya da ya kwashe tsawon shekaru baya aiki, domin taimaka ma dakarunta wajen yaki da yan ta’adda.

Kakaakin rundunar, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, inda yace rundunar ta tayar da komadar jirgin samfurin Mi-35P Helicopter ne a sansanin ta dake garin Fatakwal.

KU KARANTA: Ndume ya tubure a kan lallai sai Buhari ya tsige minista Sadiya Umar Farouk

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta tayar da komadar wani katafaren jirgin yaki
Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta tayar da komadar wani katafaren jirgin yaki
Asali: Facebook

Jirgin ya daina aiki tun a shekarar 2016, amma da gyaransa a yanzu, ya kasance kenan akwai ire irensa samfurin Mi-35P guda biyu a rundunar, kuma dukkansu a Najeriya aka gyara su.

Ko a watan da ta gabata, sai da rundunar ta tayar da komadar wani jirginta samfurin Alpha Jet NAF 455 a kwalejin horas da mayakan sama dake Kainji, jahar Neja, tuni ta tura shi filin daga.

A jawabinsa yayin kaddamar da jirgin, babban Air Marshal Sadique Abubakar ya bayyana farin cikinsa da sake mayar da jirgin a bakin aiki, sa’annan ya jinjina ma kwararrun injiniyoyinsu.

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta tayar da komadar wani katafaren jirgin yaki
Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta tayar da komadar wani katafaren jirgin yaki
Asali: Facebook

Ya cikaga da cewa yadda aka gyara jirgin a nan gida Najeriya ya nuna rundunar Sojin sama ta samu cigaba kwarai wajen kula tare da gyara jiragenta ba tare da kai su kasashen waje ba.

A cewarsa a baya sai an kai jirgi kasar waje kafin a gyara shi, kuma hakan ba karamin kudi yake ci ba, tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu rundunar ta gyara jirage da dama a gida Najeriya.

Daga karshe Sadique Abubakar ya bayyana cewa a yanzu haka duka jiragen rundunar Sojan kasa guda 23 da suka lalace sun tashi kuma sun koma bakin aiki.

Yaki da Boko Haram: Rundunar Sojan sama ta tayar da komadar wani katafaren jirgin yaki
Cibiyar dinki
Asali: Facebook

Haka zalika babban hafsan ya kaddamar da katafaren cibiyar dinki na rundunar Sojan sama a garin Fatakwal, inda suka dinka kyallen rufe fuska domin yaki da annobar Coronavirus.

Zuwa yanzu cibiyar ta dinka kyallen rufe fuska guda 40,000. Sadique yace cibiyar za ta taimaka wajen samar da dukkanin bukatun rundunar da suka shafi kayan dinki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng