Da duminsa: An samu karin mutane 7 da suka warke daga Coronavirus a Najeriya

Da duminsa: An samu karin mutane 7 da suka warke daga Coronavirus a Najeriya

- Mutane biyu dake fama da cutar Coronavirus a jihar Enugu sun warke

- Hakazalika jihar Edo ta sallami mutane biyar lokaci daya bayan gwaji sau biyu sun nuna sun samu waraka

- Adadin marasa lafiyan da ke warkewa daga cutar Korona na kara yawa a Najeriya

- Yanzu jihar Enugu ba ta da mutum ko daya mai cutar

An samu karin mutane bakwai da suka samu sauki bayan kwashe makonni suna jinya sakamakon cuta mai toshe numfashi data addabi duniya watau COVID-19.

Gwamnatin jihar Enugu ta alanta sallamar mutane biyu tal-in-tal da suka rage a cibiyar killacewarta bayan samun waraka daga cutar Coronavirus.

Mutane biyun da aka sallama mata da miji ne wadanda suka dawo Najeriya daga kasar Ingila kwanakin baya.

Kwamishanan lafiyar jihar yayin sanar da labarin sallamarsu ya yi kira ga al'ummar jihar su dage su bi umurnin gwamnati don hana yaduwar cutar.

A jihar Edo kuwa, gwamnan jihar, Godwin Obaseki, ya sanar da cewa an sallami mutane biyar masu dauke da cutar bayan gwaji ya nuna cewa babu sauran cutar cikin jikinsu.

Obaseki ya bayyana hakan ne ranar Juma'a, 17 ga Afrilu a shafinsa ta Facebook.

Yace: "Ina farin cikin sanar muku da cewa mutane biyar da suka kamu da cutar sun barranta daga Coronavirus a jiharmu. Saboda haka an sallamesu."

KU KARANTA: Mataimakin Ganduje, kwamishinoni uku da diyar Ganduje sun killace kansu

Da duminsa: An samu karin mutane 5 da suka warke daga Coronavirus a Najeriya

Da duminsa: An samu karin mutane 5 da suka warke daga Coronavirus a Najeriya
Source: UGC

Mun kawo muku rahoton hedkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC dake birnin tarayya Abuja na ci bal-bal yanzu haka.

Gobarar ta fara ne lokacin Azahar kuma anyi asarar dukiyoyi, kayan aiki, da takardu masu dimbin amfnai.

Wannan shine karo na uku da manyan ofishohin gwamnatin tarayya a Abuja ke gobara duk da cewa babu maaikata a ofishohin.

An umurci maaikatan gwamnati suyi zamansu a gida saboda dokar ta bacin da gwamnatin tarayya ta sanya a Abuja.

A ranar Larabar nan, 14 ga watan Afrilu 2020, gobara ta tashi a hedikwatar hukumar yi wa kasuwanci rijista ta kasa (CAC) da ke unguwar Maitama a birnin tarayya, Abuja.

Gobarar ta babbake hawa na karshe a ginin ofishin hukumar CAC mai bene hawa bakwai, tare da lalata muhimman kayayyaki.

Hakazalika a makon jiya gobara ta lashe ofishin akawunta janar na tarayya wacce akafi sani da baitul malin gwamnati dake Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel