Coronavirus: WHO ta nemi kasashen duniya su cika sharudda 7 kafin su janye takunkumi

Coronavirus: WHO ta nemi kasashen duniya su cika sharudda 7 kafin su janye takunkumi

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta nemi kasashen duniya dake kokarin janye dokar ta bacin da suka sanya don gudun kare yaduwar annobar Coronavirus su cika sharudda guda 7.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilu .

KU KARANTA: Wata sabuwa: Gwamna ya raba ma matasa barasa don maganin cutar Coronavirus

Tedros ya ce duk kasashen dake da nufin sassauta dokar ta bacin su tabbata sun yi haka tare da lura da takatsantsan, saboda idan har suka yi gaggawa, za’a ya ta’azzara yaduwar cutar.

Sharuddan da shugaban WHO ta gindaya ma kasashe kafin su janye dokar sun hada da:

Coronavirus: WHO ta nemi kasashen duniya su cika sharudda 7 kafin su janye takunkumi

Coronavirus: WHO ta nemi kasashen duniya su cika sharudda 7 kafin su janye takunkumi
Source: UGC

- Dole ne sai gwamnatoci sun tabbata sun dakile yaduwar cutar

- Dole ne sai kasashe sun killace duk wani mai dauke da cutar, tare da musu gwaji

- Dole sai kasashe sun binciko duk wadanda suka yi mu’amala da masu cutar

- Dole kasashe su samar da asibitoci a wuraren da annobar ta fi kamari don kiyaye dawowarta a gaba

- Dole kasashe su samar da matakan kare kariya a wuraren aiki, da makarantu

- Dole kasashe su killace tantance matafi daga kasashen waje don kare shigar cutar kasarsu

- Dole kasashe su wayar da kawunan jama’ansu tare da ilimantarsu game da illar cutar

Ita dai cutar Coronavirus na bukatar matakan kandagarki ne a yanzu sakamakon ba ta da magani, sai dai kuma ana iya kara karfin garkuwan jiki domin yaki da cutar idan ta shiga jiki.

Kamar yadda yan Hausa ke fadi idan kana da kyau sai ka kara da wanka, ga wasu daga cikin hanyoyin karfafa garkuwan jiki domin ya yaki cututtuka yayin da suka shiga jikin dan Adam;

- Kauce ma shan taba da sauran kayan hayaki

- Cin abinci mai kayan ganye

- Motsa jiki a kai a kai

- Rage kiban da ya wuce hankali

- Samun isashshen barci

- Tabbatar da tsaftar jiki da gabbai

- Rage damuwa a rai

Sai dai karfin garkuwar jiki yana raguwa da karin shekarun mutum , don haka tsofaffi basu garkuwan jiki mai karfi, don haka ake son su ci abinci masu sinadaran inganta garkuwan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel