COVID-19: Gaskiyar lamari a kan rangwame ga Maryam Sanda

COVID-19: Gaskiyar lamari a kan rangwame ga Maryam Sanda

Rahotanni na ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani ballantana WhatsApp a kan cewa gwamnatin tarayya tayi wa Maryam Sanda rangwame.

Idan zamu tuna, an yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ne bayan da alkali ya kama ta da laifin kashe mijinta.

Amma kuma sai labarin cewa shugaban kasa ya yi mata rangwame tare da wasu masu laifi a gidan gyaran halin ya bazu.

Jaridar Daily Trust ta binciko sannan ta gano cewa babu gaskiya a lamarin.

A martanin da hukumar gidajen gyaran hali ta yi a kan zancen, ta bayyana cewa har yanzu Maryam Sanda na gidan gyaran halin.

Kamar yadda takarda da mai magana da yawun hukumar gidan gyaran halin, Chucks Njoku ya fitar, ya ce: "Hankalin hukumar gidan gyaran halin ta kai ga labaran da ke yaduwa na cewa an yi wa Maryam Sanda rangwame.

"Kamar yadda labarin ya bayyana, tana daga cikin mazauna gidan da fadar shugaban kasa ta yi wa rangwame a ranar Alhamis, 19 ga watan Afirilun 2020 tare da wasu mutum 70 a gidan yarin Kuje.

COVID-19: Gaskiyar lamari a kan rangwame ga Maryam Sanda
COVID-19: Gaskiyar lamari a kan rangwame ga Maryam Sanda
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai wa Buratai hari har sansanin Ngamdu

"Hukumar na sanar da jama'a cewa wannan labarin na bogi ne kuma bashi da tushe. Wannan kuma zagon kasa ne ga kokarin fadar shugaban kasar wajen rage yawan jama'ar da ke gidan."

A yayin jawabi a taron manema labarai, Ministan cikin gidan, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana cewa akwai irin mazauna gidan gyaran halin da suka cancanci rangwamen.

Sun hada da: Masu laifin da aka yankewa hukunci amma sun wuce shekaru 60, masu laifin da hukuncinsu ya kai na shekaru uku zuwa sama amma sun kwashe watanni 6 a gidan da kuma marasa lafiya.

Marasa lafiyan dole ya kasance ya tsananta, masu tabin hankali ko kuma mazauna gidan da aka yanke wa hukuncin biyan N50,000 ba tare da wani hukunci a hade ba.

Sauran sun hada da mace mai juna biyu, mace mai yara, wadanda aka yankewa hukunci sakamakon kananan laifuka da kuma wadanda suka karba hukuncinsu kashi 75.

Njoku ya ce, Sanda bata shiga koda daya daga cikin sharuddan nan ba don haka ba za ta mora daga cikin rangwamen fadar shugaban kasar ba.

"Muna sanar da jama'a cewa har yanzu Sanda na nan a tsare kuma za a ci gaba da tsareta," yace.

Ya yi kira ga jama'a da su daina yada cewa Sanda ta mora daga cikin rangwamen fadar shugaban kasan don ba gaskiya bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel