Waiwaye: Abubuwan da baka sani ba game da annobar 1918

Waiwaye: Abubuwan da baka sani ba game da annobar 1918

- A shekarar 1918 an yi wata mummunar annoba da ta bar babban tarihi a duniya

- Duk da har yanzu babu gamsasshen bayanin tushen kwayar cutar, ta yadu a fadin duniya na shekara daya cif

- Anyi ittafakin cewa ta kama mutum miliyan 500 ko kuma daya bisa uku na mutanen fadin duniya

A shekarar 1918 an yi wata mummunar annoba da ta bar babban tarihi a duniya.

Cutar dai ta samo asali ne daga wata kwayar cutar H1N1 wacce asalinta ya fito ne daga tsuntsaye.

Duk da har yanzu babu gamsasshen bayanin tushen kwayar cutar, ta yadu a fadin duniya na shekara daya cif (1918 zuwa 1919).

A kasar Amurka, an fara samunta ne a jikin sojoji a 1918.

Anyi ittafakin cewa ta kama mutum miliyan 500 ko kuma daya bisa uku na mutanen fadin duniya.

Ta kuwa yi nasarar lashe rayuka a kalla miliyan 50 a fadin duniya amma tafi kwasa a kasar Amurka.

A kalla mutum dubu dari shida da saba'in da biyar ne suka halaka a Amurka a lokacin sakamakon cutar.

A wancan lokacin, cutar ta fi kashe mutane masu kasa da shekaru biyar, masu shekaru daga 20 zuwa 40 da kuma masu shekaru 65 zuwa sama.

Waiwaye: Abubuwan da baka sani ba game da annobar 1918

Jimillar yawan mutanen da annobar 1918 ta halaka a Najeriya da yankunan
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: An damke mutum 2 da ake zargi da yunkurin yada cutar coronavirus

Yadda cutar ta dinga halaka mutane masu matukar koshin lafiya masu shekaru 20 zuwa 40 na daga cikin abubuwan mamaki game da annobar.

Amma kuma an gano cewa cutar hada ta aka yi a dakin gwaji, hakan kuma bai sa an gano dalilin da yasa tayi barna mai tarin yawa ba.

Waiwaye: Abubuwan da baka sani ba game da annobar 1918

Waiwaye: Abubuwan da baka sani ba game da annobar 1918
Source: Twitter

Sakamakon rashin riga-kafi ko maganin cutar, hanyar hana ta yaduwa shine killace kai, killace masu cutar, tsafta, amfani da sinadaran kashe kwayoyin cuta da kuma haramta taron mutane masu yawa.

Wadannan dalilan ne suka sa annobar ta zama mafi muni a karni na 20 a fadin duniya.

A kokarin fahimta tare da gane cutar da kyau, kwararrun kungiyoyin masu bincike ne suka mayar da hankali wajen bankado sirrin cutar don shirya mata ko a nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel