Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai wa Buratai hari har sansanin Ngamdu

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai wa Buratai hari har sansanin Ngamdu

A ranar Alhamis ne mayakan Boko Haram suka kai hari a babban sansani na musamman da ke Ngamdu, inda Janar Buratai ya yada zango don ganin karshen mayakan.

Babban sansanin na musamman na nan a garin iyaka da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe.

Wannan harin ya zo ne kasa da sa'o'i 72 bayan shugaban rundunar sojin Najeriyan ya aika da sakon da ke bayyana cewa ya koma ne don yi musu kakkabar karshe.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, shugaban rundunar sojin Najeriyan ya yi bikin Easter na musamman tare da dakarun kuma ya yi alkawarin zama tare dasu har sai ya kawar da ta'addanci a yankin.

Amma kuma, a ranar Alhamis sai 'yan ta'addan suka gwada kwazonsu ta hanyar kaddamar da hari a sansanin duk da sun san cewa shugaban sojin na nan.

Sun kai harin ne a yayin da shugaban ke tare da manyan hafsoshin sojin kasar nan inda suke tsara yadda za su yi wa 'yan ta'addan kifa daya, kwala.

Majiya mai karfi daga sansanin wacce ta ce bata da damar zantawa da manema labarai, ta bayyana yadda mayakan ta'addancin suka iso a motocin yaki.

Sun bullo ne daga yankin kudu maso yammacin sansanin sannan suka bude wa sansanin wuta, majiyar tace.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kaiwa sansanin hari amma babu wanda ya rasa ransa.

Wasu daga cikin dakarun sojin ne suka samu kananan raunika.

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai wa Buratai hari har sansanin Ngamdu
Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai wa Buratai hari har sansanin Ngamdu
Asali: Facebook

KU KARANTA: COVID-19: Ministan FCT ya sanar da kwanakin bude kasuwanni

Jaridar The Nation ta gano cewa, Buratai ya umarci sojojin da su bi 'yan ta'addan.

"Shugaban rundunar sojin ya yi kira ga sojojin da su duba abinda ya faru a matsayin yunkurin dauke musu hankali a kan kokarinsu. Amma mun yi kokari sosai da muka fatattake su," majiyar tace.

Wata majiya daban ta bayyana cewa akwai yuwuwar 'yan ta'addan sun fusata ne da yadda suka ga dakarun na ta kokari don har sun fara aiki a jiya.

"Muna tsammanin cewa aikin da muka fita jiya ne ya fusata 'yan ta'addan. Kun san mun kashe musu mutanensu da muka fita jiya kuma mun kama wasu da ransu," ya sanar.

Mukaddashin daraktan hulda da jama'a na rundunar, Kanal Sagir Musa, bai samu bada amsar sakonnin da aka tura masa ba. Ya yi alkawarin kira daga baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel