Ministar Buhari ta bayyana iya adadin yan Najeriya da zasu amfana da tallafin gwamnati

Ministar Buhari ta bayyana iya adadin yan Najeriya da zasu amfana da tallafin gwamnati

Ministar kula da aukuwar bala’o’i da walwala, Sadiya Umar Farouk ta bayyana iya kimanin kashi 25 na yan Najeriya ne kawai za su ci moriyar tallafin da gwamnatin tarayya take rabawa.

Premium Times ta ruwaito ministar ta bayyana haka ne yayin da take ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Saudiyya ta baiwa mutane 1,676 marasa galihu tallafi a Kaduna da Kebbi

Sai dai Minista Sadiya ta bayyana daga yanzu ma’aikatarta za ta dinga mika kayan tallafin ga gwamnonin jahohi ne, wanda su kuma zasu raba kayayyakin ga talakawan jahohinsu.

“Ba zai yiwu kowa ya samu tallafin ba, a misali sai dai kamar kashi 25 na jama’an jahar Legas ne kadai za su iya samun tallafin, za mu iya kara adadin a gaba, amma dai iya abinda ya samu kenan a yanzu.

Ministar Buhari ta bayyana iya adadin yan Najeriya da zasu amfana da tallafin gwamnati

Ministar Buhari ta bayyana iya adadin yan Najeriya da zasu amfana da tallafin gwamnati
Source: Facebook

“Game da batun rabon kayan tallafi kuwa, za mu mayar da aikin rabon kayan ga gwamnonin jahohi don kauce ma kalubalen da muka fuskanta a baya, zamu dinga basu abincin, su kuma su raba.

“Saboda rabon abincin an tare ma’aikatanmu, an ci zarafin wasu yayin da suke gudanar da aikinsu, wannan ne tasa muka yanke shawarar mika ma gwamnoni tallafin sai su raba ma jama’a.” Inji ta.

Sai dai ministar ta ce za su fi mayar da hankali ne ga al’ummar talakawan dake birane ne, musamman ire iren wadanda suke aikin yini, kamar yadda shugaban kasa ya umarta.

“Muna da zabi, kodai mu yi amfani da rajistan talakawa da muke da shi, ko kuma mu yi amfani da tsarin talakawan dake birane, wanda za mu bi lambar rajistan asusun bankunansu watau BVN, tare da duba wadanda basu da kudin da yah aura N5,000.

“Za kuma mu yi amfani da kamfanonin sadarwa don sanin wadanda karfin sa katinsu a waya bai wuce N100 ba, wadannan ne kawai muka tabbatar talakawa ne, wadannan hanyoyi muke dubawa kafin mu yanke shawara.” Inji ta.

A hannu guda, A kokarinta na rage ma jama’a radadin halin da suke ciki a sanadiyyar annobar Coronavirus, gwamnatin jahar Legas ta bullo da tsarin ciyar da matasa dubu 100 a duk rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel