COVID-19: Mazauna Daura a jihar Katsina na korafin tsanantar yunwa

COVID-19: Mazauna Daura a jihar Katsina na korafin tsanantar yunwa

- Mazauna garin Daura sun bayyana cewa kullen da suke fuskanta a garin ya kara musu yunwa ne don basu da kudin siyan abinci

- Wani mazaunin garin mai suna Malam Lawan Usman, ya roki gwamnati da ta tallafa don fatattakar tsananin talaucin da ke damunsu

- A ranar Juma'a da ta gabata ne Masari ya bada umarnin rufe karamar hukumar Daura ta jihar Katsina

Mazauna garin Daura sun bayyana cewa kullen da suke fuskanta a garin ya kara musu yunwa ne don basu da kudin siyan abinci.

Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, Barista Ado Lalu mazaunin garin ne wanda yayi magana a madadin jama'ar garin.

"Da yawa daga cikinsu basu shirya wa kullen ba. Babu kudi balle mu siya kayan abinci mu ajiye. Da yawa daga cikinmu wadanda ke aikin kullum sun dogara da abokai da makwabta ne don ciyarwa," yace.

"A gaskiya muna bukatar tallafi daga gwamnati don samun abinci," a cewarsa.

Wani mazaunin garin mai suna Malam Lawan Usman, ya roki gwamnati da ta tallafa don fatattakar tsananin talaucin da ke damunsu.

COVID-19: Mazauna Daura a jihar Katsina na korafin tsanantar yunwa

COVID-19: Mazauna Daura a jihar Katsina na korafin tsanantar yunwa
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Yadda wasu mayunwatan 'yan Najeriya suka doka wa motar biredi da shinkafa wawaso (Bidiyo)

Wata mazauniya garin mai suna Mary Chigozie, malamar makaranta ce a kwalejin gwamnatin tarayya ta Daura, ta shawarci gwamnati da ta samar da dakin gwaji inda mazauna garin za su yi gwajin cutar.

A ranar Talata ne Gwamna Aminu Masari, ya ce an kulle garin ne don hana yaduwar muguwar cutar.

Ya ce, "An kulle Daura ne bayan mun gano cewa muguwar cutar ta shiga garin. Ina kira ga jama'a da a dinga nisantar taro da kuma wanke hannu akai-akai."

A ranar Juma'a da ta gabata ne Masari ya bada umarnin rufe karamar hukumar Daura ta jihar Katsina.

Wannan ya biyo bayan ganowa da aka yi cewa mutane uku na dauke da muguwar cutar a karamar hukumar.

Mutane ukun da suke dauke da cutar duk iyalan wani likita ne da ya rasu a jihar sakamakon samun muguwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel