Tirsasa mu aka yi muka sadaukar da albashinmu na wata biyu - Dan majalisar tarayya ya fasa kwai

Tirsasa mu aka yi muka sadaukar da albashinmu na wata biyu - Dan majalisar tarayya ya fasa kwai

- Dan majalisar tarayya Lado Suleja, ya ce 'yan majalisar wakilai sun sadaukar da albashinsu na watanni biyu ne ba da son ransu ba

- Dan majalisar ya ce shi da abokan aikinsa sun hakura da albashinsu ne bayan an tirsasa su

- Suleja ya ce da yawa daga cikin 'yan majalisar ba suyi farin cikin sadaukar da albashinsu har na watanni biyu ba

Dan majalisar wakilai mai suna Abubakar Lado Abdullahi Suleja, ya ce shi da sauran 'yan majalisar wakilai sun hakura da albashinsu don yakar COVID-19 ne ba don son ransu ba.

Dan majalisar ya sanar da hakan ne a hira da aka yi dashi a gidan rediyon da ke mazabarsa.

Ya ce an tirsasasu hakura da albashinsu ne na watanni biyu ba da son ransu ba, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Lado wanda ke wakiltar mazabar Guevera/Suleja/Tafa, ya ce duk da ya hakura da albashinsa ba da son ransa ba, ya taimakawa jama'ar mazabarsa mabukata.

Tirsasa mu aka yi muka sadaukar da albashinmu na wata biyu - Dan majalisar tarayya ya fasa kwai
Tirsasa mu aka yi muka sadaukar da albashinmu na wata biyu - Dan majalisar tarayya ya fasa kwai
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: COVID-19: Ganduje ya bada umarnin garkame jihar Kano na sati daya

Suleja ya ce da yawa daga cikin 'yan majalisar basu farin cikin hana su albashin watanni biyu da za a yi.

"Eh, mun sadaukar da albashinmu na watanni biyu ne don ci gaban Najeriya. Amma ina tabbatar da cewa da yawan mu bamu so hakan ba, wannan ce gaskiya,"

"Yadda kuke ganin ma'aikata na fusata idan aka rage musu albashi ko aka hana su ba tare da izininsu ba haka muke ji," yace.

A wani labarin mai alaka, wani kamfani a Najeriya mai suna Octo5 Holdings ya yi kokarin tallafawa gidaje 300 da ke Legas.

Kamfanin tare da wasu kamfanoni za su samar da cibiyar killacewa mai gadaje 100 a jihar don tallafawa gwamnatin jihar wajen yakar annobar Coronavirus.

Idan za mu tuna, tun bayan barkewar annobar coronavirus a kasar nan ne masu hannu da shuni suka dinga bada gudumawarsu.

Hakazalika, masu rike da mukaman siyasa ba a barsu a baya ba. Wasu sun sadaukar da rabin albashinsu inda wasu suka sadaukar da dukkan albashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel