COVID-19: Wasu ma'aurata sun saka wa dan su suna 'Sanitiser'

COVID-19: Wasu ma'aurata sun saka wa dan su suna 'Sanitiser'

- Wasu ma'aurata a kasar Indiya sun sanya wa jaririnsu suna Sanitiser saboda jinjinawa sinadarin a wannan lokacin na annoba

- Mahaifin jaririn mai suna Omveer ya ce ya jinjinawa kokarin gwamnatin kasar ta yadda ta ke samar da sinadarin ga kowa

- Omveer ya kara da bayyana matukar amfanin Sanitiser don tabbatar da kariya a yayin wannan annobar

Wani jinjiri a garin Saharanpur da ke Uttar Pradesh a kasar India, an sa mishi suna 'Sanitizer'.

Iyayen sun ce sun yi hakan ne don tunatar dasu irin halin da duniya ta taba shiga.

A yayin zantawa da manema labarai, Omveer, mahaifin jaririn ya ce yana jinjinawa gwamnati da yadda take kokarin shawo kan barkewar annobar Coronavirus a kasar, jaridar IndiaToday ta ruwaito.

"Ni da mata ta muna jinjinawa matakan da firayim minista Narendra Modi da babban minista Yogi Adityanath suka dauka a kan cutar," yace.

Ya kara da cewa 'Sanitizer' na da matukar amfani wajen hana yaduwar muguwar cutar sannan kuma a kyauta ake raba musu a fadin kasar.

COVID-19: Wasu ma'aurata sun saka wa dan su suna Sanitiser

COVID-19: Wasu ma'aurata sun saka wa dan su suna Sanitiser
Source: Original

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kano za ta rufe wasu kasuwannin jihar

Omveer ya ce sun yanke shawarar sanya wa jaririnsu sunan ne saboda su bayyana amfanin 'Sanitizer' da yadda yake kare rayuka.

"Mun saka sunan ne saboda yadda yake da amfani ga kowa a wannan lokacin gudun yaduwar cutar ta hannaye," yace.

An haifa jaririn ne a ranar 12 ga watan Afirilun 2020 a asibitin yankin Saharanpur.

A wani labari na daban, mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe jihar na mako daya.

Dokar hana shige da fice a jihar Kano din za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2020.

Kamar yadda mai bada shawara ta musamman ga gwamnan ya wallafa, ana sa ran dokar hana shige da ficen za ta yi aiki ne mako daya cif kafin a ga abinda hali yayi.

A tsawon lokacin, ba a bukatar kaiwa da kawowar jama'a ko ababen hawa a jihar. Gwamnan ya tabbatar da cewa jami'an tsaro za su damke duk wanda aka kama da laifin take dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel