Ruwan dare mai game duniya: Annobar Corona ta kashe fiye da mutum 120,000

Ruwan dare mai game duniya: Annobar Corona ta kashe fiye da mutum 120,000

Alkalumma daga kamfanin dillancin labaru na AFP sun bayyana cutar Coronavirus ta kashe fiye da mutane 120,000 zuwa karfe 12 na ranar Talata, 14 ga watan Afrilun 2020.

Alkalumma sun bayyana tun daga watan Disamba da aka samu bullar cutar a China zuwa yau, ta kashe mutane 120,013 inda kashi 70 daga ciki duk yan kasashen Turai ne.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Dan bautan kasa ya kamu da cutar Coronavirus a Ondo

AFP ta ce ta tattara wadannan alkalumma ne daga bayanan da hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO, take fitarwa ne a kullum, wanda ya nuna turawa 81,474 ne suka mutu daga cutar.

A nan gida Najeriya kuwa, Kungiyar hadakar kasashen nahiyar Turai (EU) ta bawa Najeriya tallafin Yuro miliyan hamsin (£50m) domin yaki da annobar cutar covid-19.

Ruwan dare mai game duniya: Annobar Corona ta kashe fiye da mutum 120,000

Ruwan dare mai game duniya: Annobar Corona ta kashe fiye da mutum 120,000
Source: UGC

Shugaban tawagar wakilan EU, Ambasada Ketil Karlsen, ne ya sanar da hakan yayin ziyarar da suka kai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa ranar Talata.

Yayin ziyarar, tawagar wakilan ta mika sakon jinjinar EU ga shugaba Buhari a kan kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke yi na yaki da annobar covid-19.

Da yake gabatar da jawabi, shugaba Buhari ya mika godiyarsa ga EU a kan tallafin kudin da ta bawa Najeriya domin yakar annobar cutar covid-19. Kudin ya kai naira biliyan 21.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa kudaden za su matukar taimakawa kokarin Najeriya na ganin ta shawo kan annobar cutar covid-19 kafin ta karada cikin al'umma.

"Kudin zai yi mana matukar amfani wajen sake bunkasa bangaren kiwon lafiya, Kuma mu na mika sakon ta'aziyya ga jama'ar nahiyar turai a kan barnar da annobar cutar covid-19 ta yi a nahiyar.

“Kamar yadda tarihi ya nuna, turai da sauran sassan duniya za su ga bayan wannan iftila'i," a cewar shugaba Buhari.

A wani labari kuma, kotun majistri na jahar Osun ta tura wani mutumi Akinloye Saheed zuwa gidan kaso biyo bayan wani rubutun karya da yayi a kan Coronavirus a shafin Facebook.

Daily Trust ta ruwaito Yansanda sun kama Saheed ne biyo bayan rubutun da yayi na cewa wai gwamnatin jahar Osun ta shigo da masu cutar COVID-19 zuwa jahar ne da gangan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel