FG ta fadi ranar da 'yan N-Power za su fara samun alat

FG ta fadi ranar da 'yan N-Power za su fara samun alat

A ranar Talata ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa masu cin moriyar shirin N-Power za su fara samun alawus dinsu na watan Maris daga yau, Talata.

Kakakin ministar jin dadi da walwala, Salisu Na'inna Dambatta, ne ya sanar da haka a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Talata.

Dambatta ya bayyana cewa za a fara biya matasan 500,000 da ke cin moriyar shirin a fadin Najeriya alawus dinsu daga ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wasu daga cikin matasan da ke cin moriyar shirin a jihar Kogi, sun roki gwamnatin tarayya ta biyasu alawus dinsu na watan Maris.

Da su ke magana da wakilin jaridar Daily Trust a Lokoja, ma su cin moriyar shirin sun ce biyansu alawus din a wannan lokaci zai taimaka musu wajen rage radadin matsin tattalin arziki da cutar covid-19 ta haifar.

A cikin jawabin da ministar jin dadi da walwala, Sadiya Umar Farouq, ta fitar, ta sanar da cewa ma'aikatarta ta sa hannu a kan takardun biyan matasan bisa tsarin fitar da kudade na gwamnatin tarayya.

FG ta fadi ranar da 'yan N-Power za su fara samun alat
Ma su cin moriyar shirin N-Power
Asali: Depositphotos

A cewar wani jawabi da ministar jin dadi da walwala, Sadiya Umar Farouq, ta fitar, ta bayyana cewa an janye shirin bayar da tallafin jin kai a jihohin Najeriya guda hudu.

Ta ce an dakatar da shirin a jihohin ne saboda saba ka'idojin yarjejeniyar bayar da tallafin da 'yan kwangila suka yi a jihohin.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa ba zamu iya rufe yankin arewa ba - Gwamnoni

"Gwamnatin tarayya ta bayar da kwangila ga wasu cibiyoyi don su raba kudin tallafin jin kai a jihohin Bayelsa, Akwa Ibom, Abia da Zamafara.

"An gimtse shirin a jihohin ne bisa biyayya ga tsarin bankin duniya domin tabbatar da cewa an fara biyan kudin tallafin ga jama'a a ranar 28 ga watan Afrilu ko kafin ranar," a cewar jawabin da kakakin ministar, Salisu Dambatta, ya saka wa hannu.

Ministar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta amince da jinkiri ko karbar wani uzuri wajen biyan talakawa tallafin kudin jin kai N20,000 a jihohin hudu da sauran jihohin kasa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel