Mutane 5 sun sake kamuwa da annobar Coronavirus a Najeriya, jimilla 323

Mutane 5 sun sake kamuwa da annobar Coronavirus a Najeriya, jimilla 323

Hukumar kare yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC ta sanar da samun mutane 5 da suka kamu da annobar Coronavirus a Najeriya, wanda ya kawo adadin masu dauke da cutar zuwa 323.

Daily Trust ta ruwaito zuwa yanzu dai cutar ta ratsa jahohi 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Covid-19: 'Yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnati da suka karya dokar hana taro

“Zuwa karfe 9:10 na daren Lahadi, 12 ga watan Afrilu, akwai mutane 323 da aka tabbatar suna dauke da cutar COVID-19 da aka samu rahotonsu a Najeriya, 10 sun mutu, yayin da an sallami 85.” Inji NCDC.

Jahohin da aka samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun hada da jahar Legas, mutane biyu, jahar Kwara ita ma da mutane biyu sai kuma jahar Katsina inda mutum daya ya kamu.

Ga jerin jahohin da cutar ta shiga da adadin mutanen da ta kama; Legas-176, Abuja – 56, Osun- 20, Edo- 12, Oyo- 11, Ogun- 7, Bauchi- 6, Kaduna- 6, Akwa Ibom- 5, Katsina-5 da Kwara- 4,

Sauran sun hada da Delta- 3 Enugu- 2 Ekiti- 2 Rivers-2 Ondo- 2 Benue- 1 Niger- 1 Anambra- 1 sai kuma jahar Kano-1.

Mutane 5 sun sake kamuwa da annobar Coronavirus a Najeriya, jimilla 323
Jimilla 323
Asali: Facebook

A wani labari kuma, cutar Coronavirus ta cika kwanaki 100 a duniya, wanda zuwa yanzu ta sauya tsarin duniya gaba daya sakamakon yadda ta shiga duk wani lungu da sako na duniya.

A jawabinsa na cikar Coronavirus kwanaki 100 a duniya, shugaban WHO, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa:

“A yau aka cika kwanaki 100 da hukumar WHO ta samu labarin bullar cutar Corona, wanda ya fara kamar cutar ‘Nimoniya’ amma mara sababi.”

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito tun bayan bullar cutar a kasar China, zuwa yanzu ta kama mutane 1,519,260, ta kashe mutane 88,981, a kasahen duniya 192.

Sai dai koda yake cutar ta tafka barna saosai, amma akwai wasu mutane 312,100 suka warke daga cutar a duk fadin duniya.

Alkalumma sun nuna kasar Italiya ce kan gaba wajen yawan mace mace a dalilin cutar, inda ta kashe mutane 17,669 daga cikin mutane 139, 422 da suka kamu da cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel