Boko Haram: Yadda kokarin dakarun Chadi ya taimakawa 'yan gudun hijira

Boko Haram: Yadda kokarin dakarun Chadi ya taimakawa 'yan gudun hijira

- Biyo bayan kisan dakaru 92 na kasar Chadi a ranar 23 ga watan Maris, rundunar sojin Chadi ta mayar da zazzafan martani a kan kungiyar 'yan ta'addan

- Martanin da sojojin Chadin suka yi a makonni kadan da suka gabata din ya zama mafi gawurtar harin da aka kaiwa matakan Boko Haram din a cikin shekaru 10

- Wannan lamarin kuwa ya yi matukar amfani ga 'yan gudun hijira don sun fara komawa gidajensu

Biyo bayan kisan dakaru 92 na kasar Chadi a ranar 23 ga watan Maris, rundunar sojin Chadi ta mayar da zazzafan martani a kan kungiyar 'yan ta'addan.

Hakan ya kawo sanadiyyar rasa rayukansu da kuma rasa yankunan da suka mamaye a yankin Chadin.

Martanin da sojojin Chadin suka yi a makonni kadan da suka gabata din ya zama mafi gawurtar harin da aka kaiwa matakan Boko Haram din a cikin shekaru 10.

Tun da ta'addancin ya fara, kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi suka kafa rundunar sojin hadin guiwa ta MNJTF wacce ake zargi da rashin kokarin yakar 'yan ta'addan.

Wannan ne yasa fadan ya kwashe shekaru cikin rasa rayuka da kadarori.

Boko Haram: Yadda kokarin dakarun Chadi ya taimakawa 'yan gudun hijira
Boko Haram: Yadda kokarin dakarun Chadi ya taimakawa 'yan gudun hijira
Asali: UGC

KU KARANTA: Zamfara: Rundunar 'yan sandan ta samu kwaryar jini a gidan matsafi

Kafin fusatar gwamnatin kasar Chadin, wasu majiyoyi sun ce rashin shugabanci na gari a MNJTF din da lalaci yasa wasu 'yan ta'addan ke kai hari wata kasa yayin da suke samun mafaka a wata daban.

Ana kuma zargin cewa suna zama cikin kwanciyar hankali a kasar Chadi, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Komai ya sauya a ranar 23 ga watan Maris bayan 'yan ta'addan sun kai hari ga sojojin Chadin da ke Boma a kan iyakar Najeriya da Nijar. Sun halaka sojoji 92 tare da raunata wasu da yawa.

Wannan ne babbar asarar sojoji da kasar Chadin ta taba yi tun bayan bullowar ta'addancin 'yan Boko Haram.

Wannan lamarin ne ya fusata shugaban kasar Chadi Idriss Deby, wanda shine kwamandan runduna mafi karfi ta dakaru 30,000 a kasa Chadin.

Wannan lamarin kuwa ya yi matukar amfani ga 'yan gudun hijira don sun fara komawa gidajensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel