COVID-19: Masu bincike sun bayyana lokacin da za su fitar da riga-kafin coronavirus

COVID-19: Masu bincike sun bayyana lokacin da za su fitar da riga-kafin coronavirus

- Sarah Gilbert, wata farfesa a jami'ar Oxford da ke birnin London ta ce riga-kafin cutar coronavirus zai samu nan da watan Satumba

- Gwamnatin Ingila ta ce za ta dauka nauyin hada riga-kafin matukar yayi amfani kuma za ta mika shi ga jama'a

- Farfesar ta ce tana da tabbacin cewa riga-kafin da kungiyarta ke aiki a kai zai yi matukar amfani

Sarah Gilbert, wata farfesa a jami'ar Oxford da ke birnin London ta ce riga-kafin cutar coronavirus zai samu nan da watan Satumba "in har komai ya tafi dai-dai."

Kamar yadda jaridar The Times ta ruwaito, farfesan ta ce tana da tabbacin cewa riga-kafin da kungiyarta ke aiki a kai zai yi matukar amfani.

Gwamnatin Ingila ta ce za ta dauka nauyin hada riga-kafin matukar yayi amfani kuma za ta mika shi ga jama'a.

A halin yanzu dai, an samu mutane miliyan 1.7 a fadin duniya da suka kamu da muguwar cutar, jaridar The Cable ta ruwaito.

COVID-19: Masu bincike sun bayyana lokacin da za su fitar da riga-kafin coronavirus
COVID-19: Masu bincike sun bayyana lokacin da za su fitar da riga-kafin coronavirus
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Boko Haram: Buratai ya koma Arewa maso gabas har sai ta'addanci ya kare

Mutane 103,846 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar cutar a duniya. Mutane 388,934 ne suka warke daga cutar.

Farfesar ta ce dokar kullen da aka kafa a Ingila ne yasa aka kasa gwada riga-kafin.

Kullen ne ya hana yaduwar cutar.

"Ina tunanin zai yi aikin da ake so ba kadan ba," tace.

Kamar yadda tace, "Babu wanda zai yi alkawarin cewa zai yi aiki amma kuma zai yi din. Ba mu so shekarar nan ta kai karshe babu wani riga-kafin cutar nan."

A wani rahoto na daban, an samu bullar cutar Coronavirus ta farko a jihar Kano yau Asabar, 11 ga watan Afrilu 2020, kwamishanan lafiyan jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya tabbatar da hakan.

Yanzu haka ana cikin ganawa tsakanin gwamnan da mukarrabansa. Nan ba da dadewa ba gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, zai yi jawabi ga al'ummar jihar.

A cewar majiya mai siqa, mutumin da ke dauke da cutar wani tsohon jami'in diflomasiyya ne da aka kwantar a wani asibitin kudi a Kano.

An bayyana cewa mutumin ya yi daga Legas zuwa Abuja sannan ya dira a Kano. An gwadashi ne a cibiyar gwajin dake asibitin koyarwan Aminu Kano AKTH.

Tuni an garzaya da shi dakin killace mutane a Kwanar Dawaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng