Ba zan lamunci rasa rayukan dakaruna ba - Shugaban OPSH

Ba zan lamunci rasa rayukan dakaruna ba - Shugaban OPSH

- Manjo janar Chukwuemeka Okonkwo ya bayyana cewa ba za su aminta da kisan sojoji ko wasu ma'aikata a karkashinsa ba

- Operation Safe Haven runduna ce ta jami'an tsaro da aka kafa don assasa zaman lafiya a jihar Filato da wasu sassan jihohin Kaduna da Bauchi

- Ya ce akwai bukatar shugabannin yankin su yi iya bakin kokarinsu don tabbatar da tsaron yankin

Manjo janar Chukwuemeka Okonkwo ya bayyana cewa ba za su aminta da kisan sojoji ko wasu ma'aikata a karkashinsa ba.

Manjo janar Okonkwo kwamandan Operation Safe Haven ne, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Operation Safe Haven kuwa runduna ce ta jami'an tsaro da aka kafa don assasa zaman lafiya a jihar Filato da wasu sassan jihohin Kaduna da Bauchi.

Manjo Janar din ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ziyarar da ya kai hedkwatar rundunar da ke karamar hukumar Jama'a da ke jihar Kaduna.

Okonkwo ya yi bayanin cewa rundunar za ta yi aiki da dukkan kwazonta don gamawa da 'yan ta'adda wadanda suka hana jama'a zaman lafiya.

Ba zan lamunci rasa rayukan dakaruna ba - Shugaban OPSH

Ba zan lamunci rasa rayukan dakaruna ba - Shugaban OPSH
Source: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: Buratai ya koma Arewa maso gabas har sai ta'addanci ya kare

Ya ce, a yayin da rundunar ke kokarin dasawa daga inda runduna ta baya ta tsaya, akwai bukatar shugabannin yankin su yi iya bakin kokarinsu don tabbatar da tsaron yankin.

"Don samun biyan bukata, muna bukatar dukkan masu ruwa da tsaki. Muna bukatar kai 'yan ta'addan kasa. Dole ne mu hada kanmu ba tare da duba banbance-banbance ba.

"Rundunar da ta gabata tayi iya bakin kokarinta amma akwai bukatar mu kara kwazo. Ina tabbatar muku da cewa zamu yi iya bakin kokarinmu don yakar ta'addanci a yankunan da hakan ya shafa," ya kara da cewa.

A wani labari na daban, shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya koma yankin Arewa maso gabas din kasar nan don jagoràntar yaki da 'yan ta'adda.

Legit.ng ta ruwaito hakan ne bayan takardar da daraktan hulda da jama'a na rundunar, Kanal Sagir Musa, ta fita a ranar Juma'a, 10 ga watan Afirilu.

A yayin jawabi ga dakarun da ke sansanin Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga ta jihar Borno, Buratai ya ce zai kasance tare dasu duk rintsi da tsanani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel