COVID-19: 'Yan Najeriya 13 da cutar coronavirus ta kashe a kasashen ketare

COVID-19: 'Yan Najeriya 13 da cutar coronavirus ta kashe a kasashen ketare

- A kalla 'yan Najeriya 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar coronavirus a kasashen ketare

- Daga cikinsu kuwa akwai likitoci, ma'aikatan jinya da kuma dalibai

- Dabiri-Erewa ce ta wallafa sunayen a wani bidiyo da ta saka a shafinta na Twitter

Duniya a halin yanzu tana kokarin shawo kan wannan babban kalubalen barkewar annobar coronavirus.

Sama da mutane miliyan daya be suka kamu da cutar tun bayan bullowarta a garin Wuhan da ke kasar China.

Babu wani riga-kafin cutar amma kowacce kasa na bakin kokarinta wajen samo magani.

Kwayar cutar da ke yaduwa da gaggawa ta kama 'yan Najeriya a gida da kasashen ketare.

Gwamnatin tarayya ta lissafo mutane 13 'yan Najeriya da suka rasa rayukansu a kasashen ketare sakamakon annobar.

Abike Dabiri-Erewa, shugaban hukumar 'yan Najeriya mazauna ketare, ta wallafa sunayensu a wani bidiyo da ta saki a ranar 9 ga watan Afirulu a shafinta na Twitter.

COVID-19: 'Yan Najeriya 13 da cutar coronavirus ta kashe a kasashen ketare

COVID-19: 'Yan Najeriya 13 da cutar coronavirus ta kashe a kasashen ketare
Source: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa wani tsohon sanata rasuwa

Ta yi addu'ar Ubangiji ya gafarta wa mamatan a yayin da take addu'ar ya kawo dauki ga duniya.

"Ina fatan Ubangiji ya gafarta wa 'yan uwanmu da suka rasa rayukansu a kasashen ketare sakamakon annobar coronavirus. Ubangiji ya kawo agaji kuma ya magance mana wannan cutar," ta wallafa.

Jerin sunayen 'yan Najeriyan da suka rasa rayukansu sakamakon annobar da kasashen da suka rasu.

1.Alfa Sa'adu (Ingila)

2. Carol Jamabo (Ingila)

3. Kole Abayomi, SAN (Ingila)

4. Bode Ajanlekoko (Ingila)

5. Adeola Onasanya (Ingila)

6. Ugochukwu Erondu (Ingila)

7. Chidinma Olajide (Ingila)

8. Bassey Offiong (Amurka)

9. Caleb Anya (Amurka)

10. Mmaete Greg (Amurka)

11. Akeem Adagun (Amurka)

12. Laila Abubakar Ali (Amurka)

13. Patricia Imobhio (Amurka)

Legit.ng ta ruwaito mutuwar Carol Jamabo. Ta rasa ranta ne bayan mako daya da ta kamu da muguwar cutar coronavirus.

Matar mai shekaru 56 ta rasu ne a ranar Laraba, 1 ga watan Afirilun 2020.

Ma'aikaciyar lafiya ce wacce ke da gogewa ta sama da shekaru 25 tun bayan da ta bar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel