Ban taba sanin halin da cibiyoyin lafiyar kasar nan ke ciki ya kazanta ba - Boss Mustapha

Ban taba sanin halin da cibiyoyin lafiyar kasar nan ke ciki ya kazanta ba - Boss Mustapha

- Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya koka da mummunan halin da asibitocin kasar nan ke ciki

- Ya ce ya gano mummunan halin da asibitocin kasar nan ke ciki ne bayan an zabe shi shugabancin kwamitin

- Amma kuma, ya tabbatar da cewa an fara shirin gyara tare da inganta su sakamakon barkewar annobar nan a kasar

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya koka da mummunan halin da asibitocin kasar nan ke ciki.

Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar coronavirus, ya ce ya gano mummunan halin da asibitocin kasar nan ke ciki ne bayan an zabe shi shugabancin kwamitin.

Ya sanar da hakan ne a taron da yayi da shugabannin majalisar tarayyar kasar nan a ranar Alhamis, jaridar Premium Times ta ruwaito.

"Zan iya tabbatar muku da cewa ban san mummunan halin da asibitocin kasar nan ke ciki ba har sai da na fara wannan aikin," yace.

A yayin jaddada cewa annobar ta bada damar duba halin da asibitocin ke ciki na matukar bukatar gyara, ya ce tabarbarewar asibitocin Najeriya ya ta'azzara.

Amma kuma, ya tabbatar da cewa an fara shirin gyara tare da inganta su sakamakon barkewar annobar nan a kasar.

Ban taba sanin halin da cibiyoyin lafiyar kasar nan ke ciki ya kazanta ba - Boss Mustapha

Ban taba sanin halin da cibiyoyin lafiyar kasar nan ke ciki ya kazanta ba - Boss Mustapha
Source: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi

Ya ce kwamitin da yake shugabanta zai yi kokarin ganin sun tsara yadda za a kawo gyara a bangaren.

Ya ce dukkan gudumawa za ta tafi kai tsaye ne don habakawa tare da inganta cibiyoyin lafiyar.

Mustapha ya kara da cewa, domin gaskiya da rikon amana, kwamitin ce za ta dinga karbar gudumawa tare da mika ta inda ya dace don fatattakar annobar coronavirus.

"Akanta janar din tarayya ya fitar da bayanan wasu bankuna da su kadai za a dinga tura gudumawa. Kuma dukkansu za su samu tushe ne daga babban bankin Najeriya.

"Amma kuma, duk wata gudumawa da ba ta kudi ba, za a karbeta ne a PTF, a bayyana sannan a mika ta inda ya dace," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel