COVID-19: An sake mutuwa sakamakon annobar coronavirus a Najeriya
A ranar Alhamis ne aka sake samun mutuwa sakamakon muguwar cutar coronavirus a Najeriya, jaridar The Punch ta ruwaito.
Kamar yadda cibiyar kula da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta bayyana wajen karfe 9.31 na daren Alhamis a shafinta na Twitter, an sake rasa rai sakamakon annobar.
NCDC ta ce mutane 288 ne ke dauke da cutar a fadin jihohi 17 tun bayan fara shigowar cutar Najeriya a watan Fabrairu.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Najeriya ta fara samun mai dauke da cutar ne a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Dan asalin kasar Italiyan da ya kawo cutar kuwa, tuni ya warke bayan jinyar da yayi a jihar Legas.
Bayan dan kasar Italiyan, an sake sallamar wasu masu cutar har 50.
Kamar yadda ta wallafa, "An sake samun karin mutane 14 da ke dauke da cutar a Najeriya: 13 a Legas da kuma daya a jihar Delta.

Asali: UGC
KU KARANTA: Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi
"Da karfe 9:30 na daren 9 ga watan Afirilu, akwai mutane 288 da ke dauke da cutar a Najeriya. An sallama 51 daga asibiti amma an rasa rayukan mutane 7.
"A halin yanzu, Legas na da 158, Abuja na da 54, Osun na da 20, Edo na da 12, Oyo na da 11, Bauchi tana da 6, Akwa Ibom na da 5, Ogun na da 4, Kaduna na da 5, Enugu na da 2, Ekiti na da 2, Ribas na da 2, Kwara na da 2, Delta na da 2, Benue na da 1, Ondo na da 1 sai kuma Katsina na da 1."
Har ila yau, kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya ce an sake sallamar mutane 7 da suka warke a ranar Alhamis a jihar.
Kamar yadda yace, jimillar mutanen da aka sallama a jihar Legas sun kama 39.
"A yau mu sallama mutane bakwai da suka warke daga cutar coronavirus. Gwajinsu a jere har sau biyu yana bayyana ingancin lafiyarsu.
"Wannan ne ya kai jimillar yawan wadanda aka sallama a Legas suka kai 39. Majinyatan sun hada da mace daya sai maza shida. Uku daga cikin mazan ba 'yan kasar nan bane," cewar kwamishinan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng