COVID-19: Yadda aka hana gawa shiga ma'adanar gawawwaki a Kogi

COVID-19: Yadda aka hana gawa shiga ma'adanar gawawwaki a Kogi

Jami'ai a asibitin Egbe da ke karamar hukumar Yagba ta yamma a jihar Kogi sun hana ajiye wata gawa a ma'adanar gawawwaki a kan zargi tana dauke da cutar coronavirus.

An gano cewa gawar ta iso garin ne a ranar Laraba daga Abuja.

'Yan uwan mamacin sun yi niyyar adana gawar a ma'adanar gawawwaki da ke asibitin ne kafin su shirya birneta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Amma kuma, shugaban asibitin, Dr Ola Iwarere wanda ya yi aiki da umarnin mataimaki na musamman ga gwamnan jihar a fannin tsaro, Tade Oshaloto, ya jaddada cewa ba za a bar gawar shiga asibitin ba.

Ya ce ba a san musabbabin mutuwar gawar ba kuma suna kokarin hana yaduwar coronavirus.

Ya ce bayanai game da gawar na nuna cewa ta baro Abuja ne ba tare da wata takardar shaidar lafiyarta ba.

Yana mamakin yadda motar asibitin ta bar Abuja har ta isa jihar duk da dokar hana yawo da ke aiki a jihar.

Ya kara da bayanin cewa, karamar hukumar da ke karkashin kulawarsa ta haramta taruka wadanda suka hada da bikin birne gawa har sai abinda hali yayi.

COVID-19: Yadda aka hana gawa shiga ma'adanar gawawwaki a Kogi

COVID-19: Yadda aka hana gawa shiga ma'adanar gawawwaki a Kogi
Source: UGC

KU KARANTA: Na yi luwadi ne don layar da boka ya bani ta fara aiki - Tsoho mai shekaru 58

Ya kara da cewa, dokar zaman gida ta dole na nan daram a yankin.

Kamar yadda majiya daga iyalan mamacin ta bayyana, za a birne gawar Bamigbola Olayemi ne a garin Egbe a ranakun karshen makon nan.

Amma kuma kwamishinan lafiya na jihar Ogun, Dr Saka Haruna, ya tabbatar da cewa Bamigbola Olayemi ya mutu ne ba tare da wani ciwo ba kamar yadda wasikar da ta rako gawar ta nuna.

Ya yaye tsoron ko dai coronavirus ce ta kashe mamacin, don kuwa ya ce akwai isassun shaidu da ke nuna ba cutar numfashin bace ta kashe shi.

Mamacin dattijo ne mai shekaru 83 a duniya.

Amma kuma ya jinjinawa mataimaki na musamman din ga gwamnan tare da jama'ar yankin a kan sa'idon da suka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel