Kwana 100 da bullar Corona a duniya: Ta kashe mutane 88,981 a kasashen duniya 192

Kwana 100 da bullar Corona a duniya: Ta kashe mutane 88,981 a kasashen duniya 192

A yau, annobar cutar Coronavirus ta cika kwanaki 100 a duniya, wanda zuwa yanzu ta sauya tsarin duniya gaba daya sakamakon yadda ta shiga duk wani lungu da sako na duniya.

A jawabinsa na cikar Coronavirus kwanaki 100 a duniya, shugaban WHO, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa:

KU KARANTA: Coronavirus: Yahaya Bello ya bada umarnin bude Masallatai da Coci-coci a jahar Kogi

“A yau aka cika kwanaki 100 da hukumar WHO ta samu labarin bullar cutar Corona, wanda ya fara kamar cutar ‘Nimoniya’ amma mara sababi.”

Kwana 100 da bullar Corona a duniya: Ta kashe mutane 88,981 a kasashen duniya 192

Shugaban WHO
Source: UGC

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito tun bayan bullar cutar a kasar China, zuwa yanzu ta kama mutane 1,519,260, ta kashe mutane 88,981, a kasahen duniya 192.

Sai dai koda yake cutar ta tafka barna saosai, amma akwai wasu mutane 312,100 suka warke daga cutar a duk fadin duniya.

Alkalumma sun nuna kasar Italiya ce kan gaba wajen yawan mace mace a dalilin cutar, inda ta kashe mutane 17,669 daga cikin mutane 139, 422 da suka kamu da cutar,.

Sai kasar Spain dake da matattau 15,238 daga cikin mutane 152,446 da suka kamu da cutar, kasar Amurka ce ta uku wajen yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar Coronavirus a duniya.

Inda mutane 14,817 suka mutu daga cikin mutane 432,132 da suka kamu, yayin da kasar Faransa ke biye da ita da mutuwa 10,869 a cikin masu dauke da cutar su 112,950.

Birtaniya ce ta biyar, inda mutane 7,097 suka mutu, 60,733 suka kamu, yayin da kasar China ta sanar da mutane 81,865 sun kamu da cutar, 3,335 sun mutu sai kuma 77,279 sun warke.

A wani labari kuma, gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello ya dage dokar hana bude Masallatai, coci-coci da sauran wuraren ibada domin baiwa mabiya addinai daman gudanar da ibada.

Wannan umarni tana kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labaru da sadarwa na jahar, Kingsley Fanwo ya fitar a ranar Alhamis, a garin Lokoja.

Kingslye Fanwo ya ce gwamnatin jahar ta nemi shuwagabannin addinan su tabbatar da tsare tsaren kariya daga yaduwa cutar a wuraren bautan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel