COVID-19: An killace likitocin kasar China da suka iso Najeriya

COVID-19: An killace likitocin kasar China da suka iso Najeriya

A tsaka da adawa, likitoci 15 daga kasar China sun iso Najeriya a ranar Laraba don taya yakar muguwar cutar coronavirus.

Gwamnatin tarayya ta karba wasu kayayyakin asibiti wanda rundunar likitocin suka iso da su a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kamar yadda China Civil Engineering Construction Corporation, wadanda suka dauka nauyin tafiyar suka bayyana, sun ce an taho da tan 16 na kayan gwaji, na'urorin taimakon numfashi, na'urar kashe kwayar cutar, takunkumin fuska, magunguna, safunan hannu da sauransu.

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire ne ya karba likitocin tare da kayayyakin da suka kawo.

Ya ce za a killace likitocin na kwanaki 14 wanda yayi daidai da makonni biyu don tabbatar da ingancin lafiyarsu.

"Mun san an tabbatar da lafiyarsu ta hanyar gwaji kafin isowarsu. Amma duk da haka za mu killacesu na kwanaki 14. NCDC ta je don ganin inda za a killacesu", a cewarsa.

Ehanire ya kara da cewa, "Kayayyakin da suka kawo za su taimaka ba kadan ba. A halin yanzu muna da na'urorin taimakon numfashi 50".

Jakadan kasar China a Najeriya, Zhou Pingjan, ya ce kayayyakin asibitin sun kai kimanin na dala miliyan daya da rabi. Ya kara da cewa jimillar kudin kawo su da kayan sun kai dala miliyan biyu.

COVID-19: An killace likitocin kasar China da suka iso Najeriya

COVID-19: An killace likitocin kasar China da suka iso Najeriya
Source: UGC

KU KARANTA: Na yi luwadi ne don layar da boka ya bani ta fara aiki - Tsoho mai shekaru 58

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, ta gano cewa 12 daga cikin rundunar masana kiwon lafiyan duk likitoci ne. Sauran kwararru ne a fannoni daban-daban.

Babban manajan CCECC, Michael Jiang, a wata takarda yace: "Amfanin masana kiwon lafiyan shine rakiya ga kayayyakin asibitin tare da nuna yadda ake amfani dasu.

"Za su kara da samar da bayanai tare da taimakon da ya dace. Sun kuma taho da kayan kariyar ma'aikatan lafiya isassu.

"Hakazalika, a karkashin umarnin ofishin jakadancin kasar China din, za su yi aiki tare da likitocin kasar nan tare da bada shawarwarin yadda kayayyakin ke amfani.

"Kungiyar bata zo don duba marasa lafiya a Najeriya bane."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel