Boko Haram: Gwamnatin Chadi ta yi martani mai zafi a kan zargin da ake mata

Boko Haram: Gwamnatin Chadi ta yi martani mai zafi a kan zargin da ake mata

- Gwamnatin kasar Chadi ta musanta sakin bidiyoyi da bayanai daga shugaban kasa Idris Deby, wanda yake zargin dakarun Najeriya da rashin yakar Boko Haram

- Takardar ta ce makusudin fitar da jita-jitar shine tarwatsa alakar da ke tsakanin kasashen biyu tare da hargitsa fahimtar junan da ke tsakanin hukumomin tsaronsu

- Ofishin jakadancin kasar Chadi a Najeriya ya ce, hadin kan da aka samu a yayin kafa hukumar kula da tafkin Chadi da kuma jami'an tsaron hadin guiwa abin farin ciki ne

Gwamnatin kasar Chadi ta musanta sakin bidiyoyi da bayanai daga shugaban kasa Idris Deby, wanda yake zargin dakarun Najeriya da rashin yakar Boko Haram yadda ya dace.

A takardar da ofoshin jakadancin kasar Chadi da ke Najeriya ya saki a jiya a Abuja, ta ce "mun yi watsi tare da nisanta kanmu cikin alhini a kan irin labaran da ke yawo".

Takardar ta ce makusudin fitar da jita-jitar shine tarwatsa alakar da ke tsakanin kasashen biyu tare da hargitsa fahimtar junan da ke tsakanin hukumomin tsaronsu.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ofishin jakadancin ya kwatanta Najeriya da abokiyar kasar Chadi a fannin fuskanta da habaka tattalin arziki da kuma yakar kalubalen tsaro.

Boko Haram: Gwamnatin Chadi ta yi martani mai zafi a kan zargin da ake mata

Boko Haram: Gwamnatin Chadi ta yi martani mai zafi a kan zargin da ake mata
Source: Twitter

KU KARANTA: Ka ajiye makamanka tun dare bai yi maka ba idan ba haka ba ka bakunci kiyama - Sakon Idriss Deby ga Shekau

Ya ce hadin kan da aka samu a yayin kafa hukumar kula da tafkin Chadi da kuma jami'an tsaron hadin guiwa abin farin ciki ne.

Ya kara da cewa babu abinda zai kawo rabuwar kai tsakanin kasashen biyu.

Ba za a tarwatsa kokarin tabbatar da zaman lafiya, daidaituwa da kuma tsaro a yankin.

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya yi kira ga shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, da ya fito daga maboyarshi tare da mika kanshi ko kuma a halaka shi a hakan.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da Deby ya jagoranci rundunar sojin kasar Chadi don ragargaza mayakan.

Wannan samamen kuwa ya yi ajalin a kalla 'yan ta'adda 92 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel