COVID-19: Bidiyon yadda aka fatattaki wasu 'yan Najeriya daga otal a China don gudun yaduwar cuta

COVID-19: Bidiyon yadda aka fatattaki wasu 'yan Najeriya daga otal a China don gudun yaduwar cuta

- Wasu 'yan Najeriya mazauna kasar China sun zargi 'yan sandan kasar China da tsangwama tare da hantararsu

- A bidiyon da ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani, an ga 'yan sandan na fatattakar 'yan Najeriyan daga dakunan otal don gudun kada su yada kwayar cutar coronavirus

- An ji 'yan Najeriyan na bayyana yadda 'yan kasar Chinan ke shiga kasashen Afrika suna walwala ba tare da tsangwama ba

Wasu 'yan Najeriya mazauna kasar China sun zargi 'yan kasar da fatattakarsu daga dakunan otal don gudun kada su dawo musu da cutar coronavirus.

COVID-19: Bidiyon yadda aka fatattaki wasu 'yan Najeriya daga otal a China don gudun yaduwar cuta
COVID-19: Bidiyon yadda aka fatattaki wasu 'yan Najeriya daga otal a China don gudun yaduwar cuta
Asali: Twitter

Kwayar cutar dai ta samo asali ne daga garin Wuhan na kasar China din inda ya zama annoba ga dukkan duniya. A halin yanzu kuwa ya kama a kalla mutane miliyan daya a fadin duniya.

A bangaren kasar China kuwa, ta yi nasarar shawo kan barkewar cutar amma sauran kasahen duniya na ta fama da ita, jaridar The Nation Online ta ruwaito.

COVID-19: Bidiyon yadda aka fatattaki wasu 'yan Najeriya daga otal a China don gudun yaduwar cuta
COVID-19: Bidiyon yadda aka fatattaki wasu 'yan Najeriya daga otal a China don gudun yaduwar cuta
Asali: Facebook

Wani bidiyo sabo mai cike da abun mamaki na yadda ake tsangwamar 'yan Najeriya a kasar Chinan ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani.

A bidiyon, an ga 'yan sandan kasar Chinan na korar 'yan kasuwar Najeriya daga dakin otal.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Cutar Coronavirus na dawowa jikin mutanen da aka yi musu magani, yayin da ta dawo jikin mutane 51 da suka warke a kasar Koriya ta Kudu

An ji 'yan Najeriyan suna cewa 'yan sandan Chinan, akwai 'yan kasarsu da ke yadda suka so a dukkan kasashen Afrika ba tare da tsangwama ba. Mutanen sun kara da cewa ai kasar China ce ta kawo kwayar cutar har ta shafi 'yan Najeriya.

Kamar dai yadda aka sani, cutar coronavirus ta fara bulla ne a garin Wuhan da ke kasar China tun a watan Disamban 2019.

Muguwar annobar kuwa ta ci gaba da fadawa kasashen duniya wanda hakan ya yi sanadin durkushewar tattalin arzikin kasashen duniya.

Sanannen abu ne cewa muguwar cutar ta shigo kasar Najeriya ne a watan Fabrairun 2020. Ta damki sama da mutane 200 a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel