Wata yar Najeriya mai shekaru 64 ta mutu a kasar Ingila sanadiyar cutar Coronavirus

Wata yar Najeriya mai shekaru 64 ta mutu a kasar Ingila sanadiyar cutar Coronavirus

Wata mata yar Najeriya mai shekaru 64 a duniya Mmaete Greg ta rasu a kasar Birtaniya sakamakon kamuwa da ta yi da cutar Coronavirus, kamar yadda gwajin da aka gudanar a kanta ya tabbatar.

Jaridar Punch ta ruwaito Mamete wanda mazauniyar garin Landan ce ta mutu ne a ranar Litinin, 6 ga watan Maris, kamar yadda wani dan uwanta Edoamaowo Udeme ya tabbatar ma manema labaru, kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook.

KU KARANTA: An yi rikici tsakanin Yansanda da matasa a Kaduna, mutane 5 sun mutu

Wata yar Najeriya mai shekaru 64 ta mutu a kasar Ingila sanadiyar cutar Coronavirus

Wata yar Najeriya mai shekaru 64 ta mutu a kasar Ingila sanadiyar cutar Coronavirus
Source: Facebook

Udeme ya bayyana cewa mamaciyar tana zama ne a Birtaniya, kuma a can take aiki, inda ta kwashe sama da shekaru 40 a hukumar Yansandan birnin Landan, daga bisani ta yi ritaya da kan ta.

Amma Udeme ya ce mamaciyar yar asalin kauyen Ikot Nya ne dake cikin karamar hukumar Nsit Ibom na jahar Akwa Ibom, kuma ya tabbatar da cewa matar ta yi jinya har aka shigar da ita sashin marasa lafiya dake cikin mawuyacin hali.

A kiyasin majalisar dinkin duniya, akwai sama da mutane 50,000 da suka kamu da cutar Coronavirus a Birtaniya, daga cikinsu har shugaban kasar, Boris Johnson, wanda a yanzu haka yake cikin mawuyacin hali, kuma cutar ta kashe mutane 5,000 a kasar.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa akwai magungunan gargajiya da ya yi amfani da su yayin da yake killace, wanda yace sun taimaka masa wajen warkewa daga cutar Coronavirus.

Kimanin mako daya kenan Gwamna Makinde ya sanar da kamuwa da cutar Coronavirus wanda hakan tasa ya killace kansa tare da kauce ma cudanya da jama’a don gudun kada ya harbe su da ita, amma bayan kwanaki 6 da aka sake gudanar da gwajin cutar a kansa, sai aka ga baya dauke da ita.

Jaridar TheCables ta ruwaito cikin wata hira da Makinde ya yi da gidan rediyon Fresh FM Ibadan ya bayyana cewa ya yi amfani da man habbatissaudah da kuma zuma, inda ake hada mai su duka sai ya sha, domin kara karfin garkuwan jikinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel