Gwamnatin Najeriya na tsumayin shigowar manyan jiragen ruwa 27 dauke da kayan abinci

Gwamnatin Najeriya na tsumayin shigowar manyan jiragen ruwa 27 dauke da kayan abinci

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA, ta bayyana cewa tana tsumayin shigowar wasu manyan jiragen dankaro 27 dake dauke da kayan abinci zuwa cikin gida Najeriya.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito hukumar NPA ta bayyana haka ne cikin jaridarta mai suna ‘Shipping Position’ inda tace jiragen zasu fara isowa Najeriya ne daga ranar 3 ga watan Afrilu zuwa 10 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Annobar Corona: Dan majalisar Bauchi ya sadaukar da albashinsa N476,000 domin yaki da cutar

Gwamnatin Najeriya na tsumayin shigowar manyan jiragen ruwa 27 dauke da kayan abinci
Gwamnatin Najeriya na tsumayin shigowar manyan jiragen ruwa 27 dauke da kayan abinci
Asali: UGC

Jaridar ta bayyana cewa jiragen za su shigo da fulawa, daskararren kifi, man motoci, siga, fetir, sundukai da kuma hajoji daban daban, haka zalika hukumar ta kara da cewa jirage 23 sun isa tashoshin jiragen Najeriya, a yanzu haka suna sauke kayayyaki daba daban.

Baya ga wadannan jirage 27 da ake tsumayin karasowarsu Najeriya, da jirage 23 da a yanzu haka suke sauke kaya, akwai kuma wasu jiragen 21 dake sauke kaya da suka hada da Siha, Fetir, fulawa, ababen hawa da sauran kayayya a tashoshin jiragen Najeriya.

A wani labarin kuma, wani dan majalisar dokokin jahar Bauchi dake wakiltar al’ummar mazabar Bagoro, Musa Nakwada ya bayyana albashinsa a matsayin dan majalisa, sa’annan ya sadaukar da makudan kudin domin ganin an yaki annobar Coronavirus a jahar.

Daily Trust ta ruwaito dan majalisa Musa Nakwada ya bayyana cewa ya bayar da kafatanin albashin na N476,000 ga kwamitin ko-ta-kwana da gwamnatin jahar Bauchi ta samar domin yaki da cutar Coronavirus, watau COVID-19.

A cewarsa, ya yi haka ne domin taimaka ma wannan kwamiti domin gudanar da aikinta na kare yaduwar cutar a jahar, wanda ta tilasta ma gwamnan jahar, Sanata Bala Muhammad killace kansa bayan ya kamu da cutar.

Haka zalika kungiyar lauyoyin jahar Bauchi da kuma kungiyar matasan yan kwaikwayo na jahar Bauchi sun bayar da kyautar N500,000 ga gwamnatin jahar Bauchi domin cigaba da kokarinta na yaki da cutar Coronavirus.

Jagoran kungiyar lauyoyin jahar Bauchin, Jibrin S Jibrin ya bayyana cewa sun bayar da gudunmuwar ne domin taimaka ma gwamnatin jahar wajen yaki da cutar wanda a yanzu haka ya shafi tattalin arzikin jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel