Tashin hankali: Budurwa ta kashe saurayinta ta kuma yanke masa mazakuta

Tashin hankali: Budurwa ta kashe saurayinta ta kuma yanke masa mazakuta

- Wata mata mai matsakaicin shekaru mai suna Chinenye Okoro ta tsige mazakutar saurayinta bayan hargitsi da rashin jituwa ya hada su

- Kamar yadda ganau suka bayyana, masoyan junan sun yi fada ne kuma sun saba barazanar kashe juna

- Makwabta ne suka ga tsallakawar budurwa ta katanga inda hankulansu ya kai ga gawar saurayin nata a kofar dakinshi

Wata mata mai matsakaicin shekaru mai suna Chinenye Okoro ta tashi hankulan mutane bayan ta halaka masoyinta har lahira. Ana zargin Chinenye Okoro da kashe masoyinta mai suna Ifeanyi Okoro har lahira ta hanyar tsige mishi mazakuta.

Jaridar The Punch ta gano cewa lamarin ya faru ne a yankin Akaeze da ke karamar hukumar Ivo da ke jihar Ebonyi a ranar Talata.

An gano cewa mamacin da wacce ake zargin masoyan juna ne. Sun yi fada ne sannan sun saba yi wa juna barazanar kashe juna.

Wani bakauye ne ya ga gawar mamacin a kofar dakin shi. Alamu sun nuna ya mutu ne sakamakon fizge mishi mazakuta da aka yi.

Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis da ta gabata.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar 'yan sandan, Loveth Odah ta ce "A ranar 31 ga watan Maris 2020 na wajen karfe 11 na safe wasu mutane biyu suka kawo rahoto a ofishin 'yan sandan Ivo.

KU KARANTA: Yahaya Bello ya saka a binciki kwamishinan da ake zargin ya yiwa wata budurwa fyade

"Sun bayyana cewa sun ga Chinenye Okoro ta fito daga gidansu bayan ta tsallake katanga. Hakan ne kuwa ya ja hankulansu gareta. Sun shiga gidan don sanin abinda ke faruwa, inda suka tarar da abun mamaki. Gawar Ifeanyi Okoro ce kwance a kasa wajen kofar shi.

"Bayan rahoton, jami'an 'yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru inda suka gaggauta kai gangar jikin asibitin Marthama da ke Akaeze a karamar hukumar Ivo. A nan aka tabbatar da mutuwar Ifeanyi. An adana gawar a ma'adanar gawawwaki ta asibitin kafin a kammala bincike.

"Binciken farko ya nuna cewa mamacin da wacce ake zargin masoyan juna ne kuma fada ne ya hada su. Hakan yasa Chinenye ta tsige mishi mazakuta wanda hakan yayi sanadin mutuwar shi."

Ta ce wacce ake zargin ta tsere bayan aikata aika-aikar.

"Amma kuma ana ta kokarin damko wacce ake zargin wacce za a mika a gaban kuliya don karbar hukunci," tace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel