Hukumar NCDC ta bayyana babban kalubalen da take fuskanta daga masu cutar Corona

Hukumar NCDC ta bayyana babban kalubalen da take fuskanta daga masu cutar Corona

Babban daraktan hukumar kare yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu ya bayyana babban kalubalen da suke fuskanta dangane da masu dauke da cutar Coronavirus.

Jaridar Punch ta ruwaito Dakta Chikwe ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, inda yace matsalar da suke fuskanta shi ne yadda zasu killace mutanen da suka dauke da kwayar cutar, amma babu wata alamar cutar a tattare da su.

KU KARANTA: Annobar Corona: Gwamnatin kasar Jamus ta baiwa Najeriya kyautar Yuro miliyan

Hukumar NCDC ta bayyana babban kalubalen da take fuskanta daga masu cutar Corona

Shugaban hukumar NCDC
Source: UGC

A cewar Dakta Chikwe: “Idan har mutum ba shi da wata matsala da ido za ta iya gani, amma kuma yana dauke da kwayar cutar, hakan zai sa ba zai iya zama a dakin da muka killace shi ba, don haka muke basu daman yin amfani da wayoyinsu don tuntubar yan uwa da abokan arziki.

“A yanzu mun fara kokarin samar da wani yanayi da zasu iya fita sun dan sha iska tare da sararawa a karkashin sa idon masu kula dasu, ta yadda zasu iya jure zaman har zuwa lokacin da sakamakon gwajin da aka musu zai fito.

“Babu wani takamaimen lokacin fitowa daga killacewa, har sai lokacin da sakamakon gwajin da aka musu ya fito, idan sakamakon ya nuna mutum baya dauke da shi shikenan, gaskiya wannan lokaci ne dake tattare da damuwa, don haka muke kira ga yan uwa da abokai su baiwa mutum kwarin gwiwa a wannan lokaci.” Inji shi.

A wani labari kuma, yayin da jami’an tsaro suke aikin dabbaka dokar ta baci da gwamnatin tarayya ta sanya a garin Abuja, Legas da Ogun, an samu takaddama a tsakanin wasu dakarun Sojin Najeriya da jami’an Yansanda a unguwar Nyanya na Abuja.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis a lokacin da wasu hafsoshin rundunar Sojan sama guda biyu suka tuka mota ba’a kan hanyarsu ba, har Yansanda suka tare su.

Tare su ke da wuya sai Yansandan suka nemi su koma baya, su je su bi hanyar da ta kamata, amma Sojojin suka kekashe kasa suka nuna taurin kai tare da dagewa a kan lallai ba zasu koma ba, sai dai Yansandan su basu hanya su wuce.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa: “Nan take Sojojin suka shiga zagi tare da cin mutuncin Yansandan, har da kwamandansu mai suna Azeez Idowu.” Wannan ne Yasa Yansanda suka yi kokarin kama Sojojin biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel