SGF ya mayar da martani a kan jita-jitar Buhari ya sallami Abba Kyari

SGF ya mayar da martani a kan jita-jitar Buhari ya sallami Abba Kyari

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya yi martani a kan jita-jitar da ake yadawa na cewa shugaba Buhari ya sallami shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin tarayya, Abba Kyari.

Wata wasikar sallama daga aiki na ta yawo a yanar gizo a ranar Laraba wacce ke bayyana korar Kyari daga aiki.

Amma kuma sakataren gwamnatin tarayya ya ce wasikar ta bogi ce.

A kusan makonni biyu da suka gabata ne aka gano cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasan na dauke da muguwar cutar coronavirus. A halin yanzu kuwa abu mai wahala ne a ce ga inda yake duk da cewa ya ce zai garzaya jihar Legas don killace kansa tare da karbar magunguna.

Sakataren gwamnatin tarayya, wanda ya yi martanin ta daraktan yada labarai na ofishin gwamnatin tarayyar, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa wannan rahoton ba gaskiya bane kuma ayi watsi da shi.

SGF ya mayar da martani a kan jita-jitar Buhari ya sallami Abba Kyari
SGF, Boss Mustapha da Buhari
Asali: Facebook

Kamar yadda ya bayyana, takardar karya ce don ofishin sakataren gwamnatin tarayyar bai saka hannu a kai ba.

"A haka muke fitar da takarda? An taba ganin takardar da ta fito daga sakataren gwamnatin tarayya? Ban san da wannan ikirarin ba," Bassey yace.

DUBA WANNAN: Covid-19: Wata yarinya mai shekaru 8 ta rubutawa Buhari wasika, ta bayar da tallafin N2,350

Takardar da ke ta yawo ta ce: "An sallami Abba Kyari kuma shugaban kasa ya yi alkawarin nada Alhaji Babagana Kingibe a matsayin sabon shugaban ma'aikatan.

" Shugaban kasar yana mika godiya ga Abba Kyari a kan biyayyarsa gareshi a yayin da yayi aiki da shi. Yana mishi fatan samun waraka da gaggawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel