Coronavirus ta kashe wani babban likita daga Arewacin Najeriya a kasar Birtaniya

Coronavirus ta kashe wani babban likita daga Arewacin Najeriya a kasar Birtaniya

Wani babban likitan Najeriya, dan asalin jahar Kwara amma mazaunin kasar Ingila, Dakta Alfa Sa’adu ya kamu da annobar cutar Coronavirus, kuma har ta yi ajalinsa a ranar Litinin, 30 ga watan Maris a birnin Landan.

Daily Nigerian ta ruwaito Dakta Sa’ad ya kwashe fiye da shekaru 40 yana aiki da hukumar kiwon lafiya ta kasar Birtaniya, inda har ya taba zama babban likitan birnin Landan gaba daya kafin ya yi murabus daga aiki, amma ya fito daga ritaya domin taimaka ma marasa lafiya masu cutar Corona.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana shige da fice

Coronavirus ta kashe wani babban likita daga Arewacin Najeriya a kasar Birtaniya

Alfa Sa'ad
Source: Facebook

Dan mamacin, Dani Saadu ya bayyana cewa mahaifinsa ya kwashe tsawon makonni biyu yana fama da cutar kafin ta kar shi, kamar yadda ya sanar a shafinsa na dandalin sadarwar zamani na Facebook.

“Yau da misalin karfe 7:30 ne mahaifina Dakta Alfa Saadu ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus, ya kwashe tsawon makonni biyu yana fama da cutar, ma’aikatan NHS sun yi iya bakin kokarinsu don ganin sun ceci rayuwarsa, amma ina, lokaci yayi.

“Mahaifina ya cika gwani, ya kwashe kimanin shekaru 40 yana aiki da NHS yana ceton rayuwar jama’a a nan da kuma Afirka, har zuwa lokacin da ya fara rashin lafiya, yana taimakawa wajen ceton rayukan jama’a.” Inji shi.

Jama’a da dama sun yi ta jimamin rashin Sa’adu, inda suka yi ta aika sakon ta’aziyya ga iyalansa, yan uwa da kuma abokan arziki. Sa sakon da ta aika, kungiyar likitocin Najeriya mazauna Birtaniya, MANSAG ta bayyana cewa:

“Rashin Dakta Sa’adu ya girgizamu, da dama sun bayyana shi a matsayin gwarzon namiji wanda tauraruwarsa ta haskaka duniya, kuma jigo ne a kungiyar MANSAG, kuma fitacce wajen kyawawan dabi’u” Inji ta.

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa: “Ina taya iyalan Dakta Alfa Sa’adu alhinin rashinsa, tare da jama’an Pategi da kuma jahar Kwara baki daya, marigayin ya bayar da kyakkyawar jagoranci ga yan Najeriya mazauna Birtaniya, inda ya rike shugaban kungiyar yan jahar Kwara mazauna Birtaniya.”

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya sanar da garkame jaharsa ta kowanne kusurwa domin kare yaduwar cutar Coronavirus a jahar da ma kasa baki daya, kamar yadda rahoton jaridar Sahara Reporters ta bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel