Annobar Coronavirus: Gwamnati za ta yi ma yan Najeriya 1,500 gwaji a duk rana

Annobar Coronavirus: Gwamnati za ta yi ma yan Najeriya 1,500 gwaji a duk rana

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin kara adadin mutanen da take yi ma gwajin annobar Coronavirus daga 500 zuwa 1,500 a kowacce rana, kamar yadda hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC ta bayyana.

Daily Trust ta ruwaito shugaban hukumar NCDC, Dakta Chike Ihekweazu ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron manema labaru daya gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Annobar Corona: Gwamnatin Saudiyya ta umarci Musulmai su dakatar da batun aikin Hajji

An gudanar da wannan taro ne tare da hadin gwiwar kwamitin shugaban kasa dake yaki da yaduwar cutar Coronavirus a karkashin jagoran sakataren gwamnatin Najeriya, Mista Boss Gida Mustapha.

“A makon da ta gabata mutane 500 kawai muke iya ma gwaji a duk rana, amma zuwa karshen wannan mako zamu kara adadin zuwa 1000 a duk rana, muna fatan kaiwa 1,500 zuwa mako mai zuwa.” Inji shi.

Sai dai Likitan ya bayyana cewa akwai bukatar yan Najeriya su rage neman yin gwajin domin baiwa wadanda suke da kwakkwaran bukatar yin gwajin daman yi, saboda a yanzu haka jama’a da dama suna tilasta ma kansu yin gwajin, amma kuma hukumar bata da kayan aiki.

“Yayin da basu bukatar yin gwajin suke kunno kai a kan lallai sai an musu gwajin, masu bukatar gwajin kuma suna can suna harba ma jama’a cutar a cikin al’umma, idan aka cigaba a haka, za’a cigaba da dakile ingancin tsarin aikin, kuma hakan nada hadari matuka.” Inji shi.

A wani labari kuma, karamin ministan kiwon lafiya, Dakta Olurunnimbe Mamore ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na kashe kimanin naira dubu 10 wajen gudanar da gwajin Coronavirus ta hanyar amfani da tsarin hukumar kiwon lafiya ta Duniya, WHO, dake bayar da gamsashshen sakamako.

Mamora ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake ganawa da yan jaridu a babban birnin tarayya Abuja, inda yace amma gwamnati ba wai ta damu da kashe kudin bane, tunda dai ana samun sahihin sakamako.

Da wannan ne tasa gwamnati ta dage a kan lallai ba za’a gudanar da gwajin Coronavirus a Najeriya ba sai an samu ingantattun kayan aikin yin gwajin kamar yadda hukumar WHO ta bukata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel