Abokai sun hadu sun yiwa abokinsu kisan gilla haka siddan

Abokai sun hadu sun yiwa abokinsu kisan gilla haka siddan

A jiya Alhamis ne wata kotun majistire dake Iyaganku, jihar Oyo, ta bayar da umarnin tsare wasu mutane uku da suka yiwa abokinsu dukan tsiya da har ya kai shi ga rasa ransa

Hukumar 'yan sanda ta kama Augustine Andy mai shekaru 42; Johnson Adegwu mai shekaru 21; da kuma wani dan shekara 17 da laifin hada kai suka kashe wani.

Alkalin kotun majistiren Emmanuel Idowu wanda yaki karbar korafinsu ya bukaci a kai su wajen gyaran hali dake Agodi, cikin jihar ta Oyo.

Idowu ya bayar da umarnin a kai takardun laifin nasu zuwa ga ma'aikatar shari'a ta jihar domin yanke hukunci akan lamarin.

A karshe ya daga sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Za a shiga matsanancin rashin man fetur yayin da direbobin tanka suka dakata da aiki

Wanda ya gurfanar da masu laifin, ASP Amos Adewale ya bayyanawa kotu cewa Johnson da yaro karamin sun yiwa wani mutumi dan shekara 30 mai suna Haruna Shu'aibu dukan tsiya da ya sanya ya rasa ransa.

Adewale ya zargi cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin a ranar 24 ga watan Fabrairu da misalin karfe 2 na rana a wata gona dake Ijaye, yankin Moniya dake Ibadan.

Adewale ya kara da cewa laifin nasu ya sabawa sashi na 316, kuma za ayi musu hukunci akan sashi na 319 da 324 na kundin shari'ar jihar Oyo na shekarar 2000, kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel