Yanzu-yanzu: FG za ta haramta tafiye-tafiye tsakanin jiha da jiha

Yanzu-yanzu: FG za ta haramta tafiye-tafiye tsakanin jiha da jiha

- Gwamnatin tarayya ta ce ta fara tunanin hana tafiye-tafiye tsakanin jiha da jiha ko gari da gari a kasar nan

- A wata takarda da ta fitar a ranar Alhamis, ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce yadda kasar nan ke yakar annobar na matukar aiki

- A yayin sake jaddada cewa 'yan Najeriya su kwantar da hankulansu, ministan ya ce an dauka manyan matakai kuma tsaurara

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara tunanin hana tafiye-tafiye tsakanin jiha da jiha ko gari da gari a kasar nan.

A wata takarda da ta fitar a ranar Alhamis, ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce yadda kasar nan ke yakar annobar na matukar aiki. Ya kara da cewa duk da haka kuwa akwai bukatar a kara dagewa.

A yayin sake jaddada cewa 'yan Najeriya su kwantar da hankulansu, ministan ya ce an dauka manyan matakai kuma tsaurara, hakazalika ana ci gaba da daukar irinsu don tabbatar da cewa Najeriya ta fi karfin annobar.

Kamar yadda takardar Lai Mohammed ta bayyana:

"Yan Najeriya, gaskiyar lamari shine lokaci na neman kure mana. Idan bamu dauka matakin gaggawwa ba kuma bamu yi amfani da karfi wajen tabbatar da an bi dokoki ba, ba dole ne mu iya hana yaduwar cutar nan ba.

KU KARANTA: Covid-19: Hotunan cibiyar killace masu jinyar cutuka masu yaduwa a Kano

"A don haka ne muke tunanin saka tsauraran matakai don tabbatar da an bi doka. Mu daina aika cuta daga jihar da akwai ta zuwa jihar da babu ita. Matakan sun hada da:

1. Hana shiga wata daga wata sai dai ko a lokutan gaggawa.

2. Rufe dukkanin tashoshin motoci da kuma na jiragen kasa, duk da a halin yanzu mun hana jiragen kasa yawo.

3. Amfani da maganin feshi wajen magance dukkan kwayoyin cutar da ke birane da kauyuka."

Ministan, wanda ya sanar da 'yan Najeriya a kan su shirya karbar tsauraran matakai a kokarin hana yaduwar cutar, ya sanar da manema labarai cewa gwamnatin ta san abinda ya kamata ta baiwa fifiko da kuma manyan kalubalenta.

Ya jinjinawa gwamnatocin jihohi da suka dauka tsauraran matakai wajen tabbatar da kariyar jama'a ta hanyar rufe kasuwanni da kuma hana taruka.

Mohammed ya kara da cewa, gwamnatin tarayya a shirye take wajen kara tsaurara matakai wadanda ta tabbatar za su hana yaduwar muguwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel