Jugum jugum: Ministar Abuja na zaman jiran fitowar sakamakon gwajin Coronavirus

Jugum jugum: Ministar Abuja na zaman jiran fitowar sakamakon gwajin Coronavirus

Karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Ramatu Aliyu ta bayyana cewa ta hukumar yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta gudanar da gwajin annobar nan mai toshe numfashin dan Adam, watau Coronavirus a kanta.

Jaridar Punch ta ruwaito Ramatu ta bayyana cewa ta yi mu’amala da mutanen da gwaji ya tabbatar da cewa suna dauke da cutar, hakan ne yasa wajibi ita ma ta yi wannan gwaji domin sanin matsayinta.

KU KARANTA: Gwamnan jahar Ondo ya killace kansa bayan mu’amala da gwamnan Bauchi

Jugum jugum: Ministar Abuja na zaman jiran fitowar sakamakon gwajin Coronavirus
Jugum jugum: Ministar Abuja na zaman jiran fitowar sakamakon gwajin Coronavirus
Asali: Facebook

Zuwa yanzu dai hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta bayyana cewa daga cikin mutane 46 da aka samu suna dauke da cutar Corona, mutane 8 a babban birnin tarayya Abuja su ke, daga cikinsu har da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

Hajiya Ramatu ta bayyana haka ne a shafinta na dandalin sadarwar zamani na Twitter a daren Laraba, inda tace: “Yanzu na bayar da abubuwan da ake bukata na yin gwajin COVID-19, lafiya na kalau dai, kuma tun a jiya na kebance kai na saboda na yi mu’amala da mutanen da suka kamu da cutar.

“Don haka kowa yak are kansa, kuma a dauki matakan riga kafi kamar yadda hukumar NCDC ta bayyana. A yayin da nake a killace, ina aiki tare da shuwagabannin kananan hukumomin Abuja 6 wajen kariya da wayar da jam’a.” Inji ta.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya shiga halwa inda ya kebance kansa domin kauce ma yada cutar Coronavirus wanda ake tunanin zai iya kamuwa da ita sakamakon mu’amalar da ya yi da gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad.

Baya ga shiga halwa, gwamnan ya soke dukkanin sha’ani da suka shafe shin a tsawon kwanaki 14, wannan ya biyo bayan gwajin da aka yi ma Bala Muhammad, wanda sakamakon ya nuna Bala ya kamu da cutar.

Wata majiya daga fadar gwamatin jahar ta bayyana cewa: “Gwamna Akeredolu yana Abuja a makon da ta gabata, inda ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da sauran gwamnonin APC, kuma a lokacin Coronavirus ta fara yaduwa.

“Don haka ya dauki matakin kandagarki bayan an sanar da sakamakon gwajin da aka yi ma gwamnan jahar Bauchi, dole tasa ya killace kansa saboda babu tabbacin ko ya kusanci Gwamna Bala Muhammad a Abuja ko akasin haka.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel