Rundunar soji ta kwace miyagun makamai daga wajen 'yan bindiga a Agatu
- An samu miyagun makamai masu tarin yawa daga garuruwa biyu na karamar hukumar Agatu da ke jihar Benue bayan jami'ai daga rundunar sojin Najeriya sun kai samame
- Rundunar Operation Whirl Stroke tare da hadin guiwar rundunar sojin saman Najeriya a tare da bataliya ta 72 ne a sa'o'in farko na ranar Litinin suka kai samame a garuruwan Odogoke da Odejo
- Onyeuko ya kara da cewa tuni dai komai ya koma daidai a yankin sannan tsaro ya dawo. Ya kara da cewa har yanzu dai sojin na sintiri a yankin don tabbatar da wanzuwar lumana da daidaituwa
An samu miyagun makamai masu tarin yawa daga garuruwa biyu na karamar hukumar Agatu da ke jihar Benue bayan jami'ai daga rundunar sojin Najeriya sun kai samame a ranar Litinin.
Mukaddashin daraktan yada labaran tsaro, Birgediya Janar Bernard Onyeuko a wata takarda ya ce, "Jami'an rundunar Operation Whirl Stroke tare da hadin guiwar rundunar sojin saman Najeriya a tare da bataliya ta 72 ne a sa'o'in farko na ranar Litinin suka kai samame a garuruwan Odogoke da Odejo na karamar hukumar Agatu ta jihar Benue bayan barnar da 'yan bindiga suka yi a ranar 23 ga watan Maris din 2020. A nan take kuwa 'yan bindigar suka tsere tare da barin yankin inda suka bar makamansu.
"Makaman da aka samu sun hada da bindiga mai carbi guda biyu, carbin harsashi guda hudu, bindiga kirar fiston daya da sauransu," takardar tace.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Tashin hankali a fadar shugaban kasa bayan Gwamnan Bauchi ya killace kansa
Onyeuko ya kara da cewa tuni dai komai ya koma daidai a yankin sannan tsaro ya dawo. Ya kara da cewa har yanzu dai sojin na sintiri a yankin don tabbatar da wanzuwar lumana da daidaituwa a yankin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne wasu garuruwa biyu a karamar hukumar Agatu din suka yi kare-jini, biri-jini a kan wani tafkin kiwon kifi ta yadda har mutane biyar suka rasa rayukansu.
Garuruwan masu suna Aila da Egba sun dau hukunci a hannunsu inda suka dinga fada da juna sannan daga baya suka dorawa sojojin laifin kashe fadan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng