Boko Haram: Dakaru 70 rundunar sojin Najeriya ta rasa a ranar Litinin

Boko Haram: Dakaru 70 rundunar sojin Najeriya ta rasa a ranar Litinin

A kalla dakarun sojin Najeriya 70 ne suka rasa rayukansu sakamakon fatattakar tawagar 'yan ta'addan Boko Haram da suka yi a jihar Borno da ke yankin Arewa maso yamma na kasar nan, kamar yadda wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar a ranar Talata.

Mayakan Boko Haram din sun harba makami mai linzami a kan wata mota ce da ke dauke da dakarun a yayin da motar ke tafiya a kusa da kauyen Gorgi a jihar Borno, kamar yadda wasu sojoji biyu suka sanar da AFP tare da bukatar sakaya sunayensu.

"Wannan babban rashi ne don a kalla dakaru 70 ne suka mutu a wannan karon," daya daga cikin sojin yace.

'"Yan ta'addan sun saita motar da ke dauke da sojojin ne sannan suka sakar mata makami mai linzamin inda ya kama da wuta tare da kashe dukkan dakarun," dayan sojan ya sanar.

"A halin yanzu, gawawwakin dakarun 70 an samosu kuma sojoji da yawa sun samu raunika yayin da wasu suke hannun 'yan ta'addan don garkuwa dasu." yace.

Boko Haram: Dakaru 70 rundunar sojin Najeriya ta rasa a ranar Litinin
Boko Haram: Dakaru 70 rundunar sojin Najeriya ta rasa a ranar Litinin
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin jiragen da rufe filayen jirage ba zai shafa ba - Sirika

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya ya sanar da AFP cewa ba zai iya tsokaci akan wannan harin ba.

Rundunarsu ta bar yankin babban birnin Maiduguri din don za su kai hari sansanin 'yan ta'addan ne, kamar yadda wani dan taimakon kai da kai ya sanar da AFP.

Bangaren ISWAP dai sun rabe da mayakan Boko Haram tun a 2016 kuma sun mayar da hankali ne wajen harar rundunar soji, kwashe makamai da kuma halaka tawagar jami'an tsaro.

An zargi kungiyar da ci gaba fda harar farar hulla tare da yin garkuwa da jami'an tsaro masu tsare kan hanyoyi.

Al'amuran 'yan ta'addan da ya dau a kalla shekaru 10 ya halaka mutane 36,000 kuma ya tarwatsa mutane a kalla 1.8 miliyan daga gidajensu a yankin Arewa maso gabas na kasar nan.

Mayakan sun kara da mamaye yankunan kasashen da ke da makwabtaka da Najeriya wanda hakan yasa aka hada jami'an tsaro hadin guiwa tsakanin kasashen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel