Coronavirus shaidan ne, ba zamu daina zuwa coci da masallatai ba - Shugaban kasar Tanzania

Coronavirus shaidan ne, ba zamu daina zuwa coci da masallatai ba - Shugaban kasar Tanzania

Wani bidiyon shugaban kasar Tanzania, John Joseph Magufuli ya bayyana inda yake kokarin yin wasa da rayukan jama'ar kasarsa duk da kuwa barkewar annobar coronavirus a duniya.

Kasashen duniya na ta kokarin ganin sun bi ka'idoji tare da gujewa duk wata hanyar yaduwar cutar. Hakan yasa ake ta garkame majami'u, mashaya da sauran wuraren shakatawa.

A lamarin kasar Tanzania kuwa ba hakan bane, don kwata-kwata sun shan banban da kowa. Shugaban kasar ya ki baiwa mabiyansa umarnin bin ka'idoji tare da matakan yaka ko hana yaduwar cutar.

Ya yarda cewa maganin cutar na tafe ne daga coci kuma cutar shaidan ce da tazo don hana su bautar Ubangiji, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

An nadi bidiyon shugaban kasar yana cewa: "Ba zamu rufe wani wajen bauta ba. A nan ne magani sahihi yake. Corona ce shaidanin kuma ba za ta yi tasiri a jikin Yesu ba".

Coronavirus shaidan ne, ba zamu daina zuwa coci da masallatai ba - Shugaban kasar Tanzania

Coronavirus shaidan ne, ba zamu daina zuwa coci da masallatai ba - Shugaban kasar Tanzania
Source: Twitter

KU KARANTA: Tashin hankali a fadar shugaban kasa bayan Gwamnan Bauchi ya killace kansa

A wani labari na daban, mun ji yadda sakamakon gwajin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Covid-19 ya nuna cewa shugaban baya dauke da kwayar cutar kamar yadda Thisday ta ruwaito.

Hukumar NCDC ta sanar da shugaban kasar cewa ba ya dauke da kwayar cutar a safiyar yau a Abuja. A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar kamar yadda sakamakon ya nuna a ranar Litinin.

Kyari ya tafi Jamus a ranar Asabar 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu jami'an kamfanin Siemens a binrin Munich a kan shirin fadada aikin wutan lantarki a Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa ya hallarci taron da aka gudanar a kan annibar Covid-19 a Najeriya a ranar Lahadi inda a nan ne ya fara tari. Daga bisani ya mika kansa domin a yi masa gwaji kuma a jiya Litinin aka sanar da shi sakamakon gwajin.

Tuni dai Kyari ya killace kansa tun bayan da ya samu sakamakon gwajin. Bayan fitowar sakamakon gwajin na Abba Kyari ya nuna yana dauke da cutar, an shawarci Buhari ya yi gwajin shima kuma aka gwada shi aka gano baya dauke da kwayar cutar kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa TheCable.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel