Yadda 'yan bindiga suka kai hari kauyuka 10 a jihar Benue

Yadda 'yan bindiga suka kai hari kauyuka 10 a jihar Benue

- A kalla kauyuka 10 ne a gundumar Mbaiikyor da ke karamar hukumar Kwande ta jihar Benue a daren lahadi suka fuskanci mummunan hari

- Shugaban kwamitin rikon kwarya na yankin, Tertsua Yarkarn, ya ce har yanzu dai ba a san ko mutane nawa bane abin ya shafa don jama'a da yawa sun gudu tare da barin gidajensu

- Amma kuma, da aka tuntubi kwamandan rundunar Operation Whirl Stroke, Manjo janar Adeyemi Yekini, ya karyata harin

A kalla kauyuka 10 ne a gundumar Mbaiikyor da ke karamar hukumar Kwande ta jihar Benue a daren lahadi suka fuskanci mummunan hari.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa maharan sun isa yankin ne da karfe 7 na yammaci inda suka dinga harbe-harbe tare da kona gidajen jama'a.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na yankin, Tertsua Yarkarn, ya ce har yanzu dai ba a san ko mutane nawa bane abin ya shafa don jama'a da yawa sun gudu tare da barin gidajensu.

Yarkarn, wanda tun farko ya bayyana cewa ana shirin kawo musu harin, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa wannan na daga cikin mummunan harin da aka taba kawowa yankin a tarihin ta'addanci.

Yadda 'yan bindiga suka kai hari kauyuka 10 a jihar Benue
Yadda 'yan bindiga suka kai hari kauyuka 10 a jihar Benue
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tashin hankali a fadar shugaban kasa bayan Gwamnan Bauchi ya killace kansa

Ya kara da cewa, "Gundumar Mbaiikyor ta fuskanci mummunan hari daga fulani makiyaya. Muna bukatar tallafin kaya da na jami'an tsaro." ya sanar a sakon karta kwana da ya tura.

Amma kuma, da aka tuntubi kwamandan rundunar Operation Whirl Stroke, Manjo janar Adeyemi Yekini, ya karyata harin. Ya jaddada cewa akwai kungiyoyin tsaro har kashi biyu tare da jami'ansu a wannan bangaren.

Yekini yace, "Wadannan duk jita-jita ne. Akwai rundunar jami'an tsaro a wajen kuma labarin kagagge ne,"

Ya kara da cewa rundunarsa ta dinga bibiyar jita-jitar harin da ake zargin za a kawo yankin a kwanaki uku da suka gabata. Mun hada da runduna ta 73 ta soji a jihar Taraba.

Amma kuma shugaban kwamitin rikon kwaryar ya jaddada cewa maharan sun yi watsa-watsa da kauykansu. Hakazalika maharan sun kai hari a garin Tyungu Timbee a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel