Jerin jiragen da rufe filayen jirage ba zai shafa ba - Sirika

Jerin jiragen da rufe filayen jirage ba zai shafa ba - Sirika

- Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama ya ce filayen jiragen saman Najeriya har yanzu suna bude amma ga jiragen saukar gaggawa na kaya da kuma aiyukan taimakon jama'a

- A matsayin hanya da kokarin gwamnati na hana yaduwar cutar coronavirus, gwamnatin tarayya ta haramta tashi da saukar jirage a filayen sama manya biyu na kasar nan

- Dukkan fiilayen jiragen saman za su kasance a rufe na makonni hudu. Wadanda ke dan bukatar saukar ko tashi sai sun nemi amincewar ministan

Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama ya ce filayen jiragen saman Najeriya har yanzu suna bude amma ga jiragen saukar gaggawa na kaya da kuma aiyukan taimakon jama'a.

A matsayin hanya da kokarin gwamnati na hana yaduwar cutar coronavirus, gwamnatin tarayya ta haramta tashi da saukar jirage a filayen sama manya biyu na kasar nan. Sun hada da filayen sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas da kuma na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Amma kuma kamar yadda ministan ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Litinan, Sirika ya ce akwai wadanda wannan dokar bata shafa ba don za su iya amfani da filayen jiragen matukar an amince musu.

"An rufe dukkan filayen jiragen sama na tsakanin kasa da kasa na makonni hudu, amma banda jiragen gaggawa da kuma na kaya," ya rubuta.

Jerin jiragen da rufe filayen jirage ba zai shafa ba - Sirika

Jerin jiragen da rufe filayen jirage ba zai shafa ba - Sirika
Source: UGC

KU KARANTA: Manyan kasashen duniya guda goma da suka fi farin ciki da jin dadin rayuwa

Dukkan fiilayen jiragen saman za su kasance a rufe na makonni hudu. Wadanda ke dan bukatar saukar ko tashi sai sun nemi amincewar ministan.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta haramta sauka da tashin jiragen kasar nan zuwa wasu kasashe 15 wadanda suka hada da Ingila, Amurka, China da kuma kasar Italiya.

A wani labari na daban, daya daga cikin ma'aikata a ofishin mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya kamu da cutar nan mai kisa ta Corona, mai magana da yawun mataimakin ne ya bayyana haka jiya Juma'a da yamma .

Duk da dai cewa ofishin na Pence bai bayyana ainahin sunan mutumin ko kuma mukamin da yake rike da shi ba, amma dai sanarwar ta bayyana cewa shine mutum na farko da ya kamu da cutar a fadar shugaban kasar, kuma hakan ya zo ne a lokacin da ake cikin damuwa dangane da lafiyar 'yan siyasa na birnin Washington, manyan ma'aikatan gwamnati da kuma wadanda suke yi musu aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel