Rundunar 'yan sanda ta damke mutumin da ya kashe kwarton matarsa

Rundunar 'yan sanda ta damke mutumin da ya kashe kwarton matarsa

- Wani mutum mai shekaru 35 mai suna Habeeb Kasali ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Ogun a kan laifin da ake zarginsa na halaka wani Bamidele Johnson

- An kama wanda ake zargi da kisan kan ne bayan samun bayanai daga ofishin 'yan sanda na yankin Igbesa daga 'yan uwan mamacin

- Bayan ganowa cewa kwarton matar shi din ya rasu, sai wanda ake zargin ya tsere. Da gaggawa kuwa DPO din ofishin 'yan sanda na Igbesa ya tura jami'ansa inda suka damko shi

Wani mutum mai shekaru 35 mai suna Habeeb Kasali ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Ogun a kan laifin da ake zarginsa na halaka wani Bamidele Johnson mai shekaru 32 a duniya.

Kasali yayi hakan ne sakamakon zargin Johnson da yake da lalata da matarsa.

An kama wanda ake zargi da kisan kan ne bayan samun bayanai daga ofishin 'yan sanda na yankin Igbesa daga 'yan uwan mamacin.

Kamar yadda 'yan uwan mamacin suka sanar, rikici ya sarke tsakanin wanda ake zargin da kuma mamaci a yankin Totowu. Fadan ya fara ne bayan da wanda ake zargin ya tare mamacin tare da kara ja mishi kunne a kan kwartanci da matarsa.

Rundunar 'yan sanda ta damke mutumin da ya kashe kwarton matarsa

Rundunar 'yan sanda ta damke mutumin da ya kashe kwarton matarsa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Babbar magana: An nade kafet din Masallacin Harami a Saudiyya saboda coronavirus

A wannan halin ne wanda ake zargin yayi amfani da almakashi ya sokawa mamacin sau ba adadi a kirji, ido da wuya. Hakan ne kuwa yasa mamacin ya fadi kasa rai a hannun Allah. A take aka hanzarta kai shi asibitin Crest da ke titin Isuti a Egan da ke jihar Legas inda aka tabbatar da cewa ya rasu.

Bayan ganowa cewa kwarton matar shi din ya rasu, sai wanda ake zargin ya tsere. Da gaggawa kuwa DPO din ofishin 'yan sanda na Igbesa ya tura jami'ansa inda suka damko shi.

Gawar mamacin tana babban asibitin Ota don duba musabbabin mutuwarsa.

A halin yanzu, Kwamishinan 'yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson ya bada umarnin mayar da wanda ake zargin zuwa sashi na musamman na binciken manyan laifuka don bincike da gurfanarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel