Coronavirus: Akwai yuwuwar garkame majalisar tarayya a wannan makon
- A yayin da aka ci gaba da samun barkewar cutar Covid-19 a Najeriya, akwai yuwuwar a garkame majalisar tarayyar kasar nan
- Tuni dai jami'an tsaron da ke aiki da majalisar aka bukacesu da su hana baki shiga farfajiyar majalisar tun daga ranar Talata da ta gabata
- Wani babban jami'i a majalisar yace akwai yuwuwa mai yawa ta garkame majalisar a makon nan
A yayin da aka ci gaba da samun barkewar cutar Covid-19 a Najeriya, akwai yuwuwar a garkame majalisar tarayyar kasar nan, kamar yadda jaridar Punch ta bayyana.
Tuni dai jami'an tsaron da ke aiki da majalisar aka bukacesu da su hana baki shiga farfajiyar majalisar tun daga ranar Talata da ta gabata.
Wasu sanatoci wadanda suka zanta da wakilan Punch, sun yi bayanin cewa abinda ya hana a rufe majalisar shine saboda babu mai cutar da aka samu a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.
Amma kuma, bayan sa'o'i kalilan sai ma'aikatar lafiya ta tarayya ta bayyana cewa an kara samun mutane 10 da ake zargin su da samun cutar kuma uku daga ciki suna Abuja yayin da bakwai ke Legas.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Yadda al'amura ke gudana a gidan tsohon sarki Sanusi II Legas bayan mako guda
Daya daga cikin 'yan majalisar daga yankin Kudu maso Yamma wanda ya bukaci a sakaya sunansa yace, "A halin yanzu da aka samu cutar a Abuja, bamu da wani mataki da ya wuce bukatar rufe zauren majalisar a ranar Talata mai zuwa."
Wani sanata kuwa daga yankin Arewa ta tsakiya wanda ya bukaci a sakaya sunansa, yace tunda wasu 'yan majalisar sun dawo daga kasashen ketare a makon da ya gabata kuma an bukacesu da su killace kansu na makonni biyu sannan ayi musu gwajin cutar, toh babu dalilin bude zauren majalisar.
"An samu masu cutar har mutane uku a Abuja, don haka babu dalilin da zai sa a bude majalisar. Zai fi idan aka rufe ta duka," yace.
Wani babban jami'i a majalisar yace akwai yuwuwa mai yawa ta garkame majalisar a makon nan.
Ya ce; "Yan majalisar sun mika bukatarsu ga hukumar kuma muna duba hakan. Akwai yuwuwar rufe zauren majalisar dukanshi saboda gujewa yaduwar cutar."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng