Coronavirus: Sarkin Daura ya ja jami'in dubban mutane don rokon Ubangiji
- Jama'ar Daura da ke jihar Katsina a ranar Asabar sun fada addu'o'i don neman kariya daga sabuwar mugunyar cutar coronavirus
- Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq, ya jagoranci mazauna garin sallah ta musamman don rokon Ubangiji kariya daga cutar
- Yayi kira ga jama'a da su tsananta addu'ar neman kariya daga cutar da sauran cutukan da ke kashe jama'a
Jama'ar Daura da ke jihar Katsina a ranar Asabar sun fada addu'o'i don neman kariya daga sabuwar mugunyar cuta r coronavirus.
Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq, ya jagoranci mazauna garin sallah ta musamman don rokon Ubangiji kariya daga cutar.
Sarkin mai shekaru 84 ya ja sallar ne a farfajiyar fadarsa. Ya bukaci mazauna garin da su kalla muguwar cutar da wata jarabawa daga Allah.
Yayi kira ga jama'a da su tsananta addu'ar neman kariya daga cutar da sauran cutukan da ke kashe jama'a.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Manyan kasashen duniya guda goma da suka fi farin ciki da jin dadin rayuwa
Sarkin ya kwatanta wannan cutar da hatsarin da yafi na Boko Haram, ya kuma yi addu'ar cewa Ubangiji ya kawo karshen wannan masifa da gaggawa.
Ya yi umarni ga dukkan malaman makaratun allo da na Islamiyyu na kowacce mazhaba a kan su rufe makarantunsu tare da biyayya ga dukkan umarnin gwamnati.
A wani labari na daban, a yayin da duniya ta rike ta kuma dimauce akan cuta mai kisa da ta addabi kowacce kasa ta duniya wato Coronavirus, zai zama kamar ba yanzu ne ya kamata a bayyana kasashen da suka fi farin ciki a duniya ba.
Amma dai duniya ta fitar da rahoton kasashen da suka fi farin ciki a duniya a shekarar 2019, inda ta bayyana kasar Finland a matsayin ta farko a bangaren farin ciki da jin dadin rayuwa.
Haka kuma rahoton yana duba kasashe akan abubuwa guda shida da suka hada da tattalin arziki, jin dadin rayuwa, harkar lafiya, walwala, kirki da mutunci tsakanin al'umma, rashin cin hanci da rashawa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng