Yaro mai shekaru 4 mara hannaye wanda ya ki bara sai makaranta

Yaro mai shekaru 4 mara hannaye wanda ya ki bara sai makaranta

Abdullahi Umar yaro ne karami mai shekaru hudu a duniya. An haife shi ne babu hannaye kwata-kwata. Ya fara gwagwarmaya ne tun lokacin da yake karamin shi.

Bayan haihuwar shi a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa a ranar 25 ga watan Maris din 2015, mahaifin shi Musa Umar bai bata lokaci ba ya kori jaririn da mahaifiyar shi sakamakon zarginta da maita.

Umar ya ce abu daya zai sa ya dawo da matar shi dakinta shine idan ta yadda jaririn da ta haifa a kogi, lamarin da mutane da yawa suka goyi baya a yankin.

Wannan lamarin kuwa ya jawo babbar matsala a auren. Tsokaci kuwa kala-kala ya biyo baya ballantana daga wadanda suka bata shawarar kashe yaro.

Amina, mahaifiyar Abdullahi ta kusan bin shawarar mutane amma sai mahaifiyarta ta hana ta. A maimakon hakan, sai ta basu matsuguni a gidanta inda take taimaka mata wajen kula da jinjirin.

"Ko kawayena na kusa sun ce bai kamata in bar yaron da rai ba duk da cewa ina son shi. Zai yi rayuwa ne mai cike da nakasa," ta ce.

Halin da Abdullahi yake ciki ba irin na kowa bane. Bashi da damar da zai rike komai. A maimakon hakan, ya dogara ne ga kafafunsa don yin dukkan al'amuran rayuwarshi. Ba wahala kadai wannan lamarin ya bashi ba a rayuwa, lamarin ya hana shi shiga cikin yara masu irin shekarun shi.

Wakilin jaridar The Nation ya ziyarci makarantar da Abdullahi yake da kuma gidan kakar shi inda mahaifiyarshi take a Toto da ke jihar Nasarawa. An ga yadda karamin yaron ke da kwarin guiwar rayuwa mai amfani duk da kuwa irin halin da yake ciki na nakasa.

KU KARANTA: Yadda muke sayar da 'yan Najeriya a matsayin bayi a kasar Libya

A shekaru hudun da yake, mahaifiyar shi ta so dinga bara dashi don neman sadaka amma yaron ya ki amincewa ayi amfani da nakasar shi don samun kudi.

A maimakon hakan, sai ya fara makaranta duk da iyayen shi basu so ba don tunanin yadda yaro mara hannuwa zai iya karatu.

A yayin zantawa da shugaban makarantar da yaron yake. Ta ce, "Wata kawata ce ta sanar dani labarin nakasar yaron da kuma yadda yaki yarda ayi bara dashi. An sanar dani cewa yana kuka tare da bukatar zuwa makaranta amma mahaifiyar shi ta ce bata da halin kaishi makaranta.

"Na sake bincikawa sannan na bukaci mahaifiyar da ta kawo shi. A halin yanzu Umar yana amfani da kafafun shi wajen rubutu. Yaro ne mai hazaka sosai.

"Babbar cuta mai nakasa mutum ita ce jahilci. Umar yaro ne mai hazaka kuma Ubangiji ya nufa zai zo makaranta ta. Yana da hazaka fiye da sauran yara marasa nakasa,"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel