Daga gadi na fara amma yanzu yanzu na mallaki kamfanin hakar man fetur da iskar gas - AD Patrick

Daga gadi na fara amma yanzu yanzu na mallaki kamfanin hakar man fetur da iskar gas - AD Patrick

- AD Patrickson ya bayyana irin aikin gadin da ya dinga amma sai Ubangiji ya daukaka shi zuwa mamallakin kamfanin mai da iskar gas

- Labarin ba a nan ya tsaya ba, matashin ya dage da aiki tukuru ne kafin ya cimma mafarkinsa kuma ya samu cikar burinshi

- Patrickson ya ce ya zama mutum na farko dan asalin yankinsu da ya mallaki kamfanin hakar man fetur da iskad gas ba tare da tallafin wani kwararre ba

Wani mutum mai sun Patrickson ya bayyana labarin nasararshi mai cike da ban al'ajabi. Ya zama mamallakin kamfanin man fetur da iskar gas bayan shekarun da ya dauka yana gadin wajen hakar man fetur din.

Kamar yadda ya bayyana, babu abinda ke hana mutum samun nasara matukar yana sha'awar abinda yake yi kuma ya dage da aiki tukuru. Ya ce ya saka dukkan kokarin shi ne don cimma mafarkin shi da burin shi. Ya ce sha'awar nasara ce ta sa ya ci gaba da karatu. Bayan nan kuwa, kwararre a hakar man fetur din ya ce yana tallafawa tare da ba kasar shi gudumuwa.

Daga gadi na fara amma yanzu yanzu na mallaki kamfanin hakar man fetur da iskar gas - AD Patrick

Daga gadi na fara amma yanzu yanzu na mallaki kamfanin hakar man fetur da iskar gas - AD Patrick
Source: Twitter

KU KARANTA: Kisan sifetan 'yan sanda: Jama'ar Imasai sun fara gudun hijira

Kasar Kamaru kuwa ta amfana dashi sakamakon wannan burin nashi. A yanzu kuwa da aiki tukuru ya biya, ya zama mutum na farko a kasar shi da ya mallaki kamfanin hakar man fetur da iskar gas a kasar.

A kalaman shi, ya shawarci duk wani mai buri da fatan samun nasara da ya dage don tabbas nasara daga Ubangiji take kuma za ta samu duk wanda ya nema.

A wani labari na daban, an samu mugun hargitsi ne a ranar Asabar a garin, sakamakon fada tsakanin jami’an tsaron iyakar kasa da wasu mazauna yankin wanda ya jawo kisan sifetan ‘yan sandan.

Amma kuma ‘yan sandan sun ce an kama mutane takwas da ke da hannu a wannan kisan, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Amma kuma a madadin mazauna yankin, shugaban yankin wanda ake kira da Atunluse na Imasai, Chief John Odu, da kuma wani mataimaki na musamman ga tsohon gwamna Ibikunle Amosun, Raheem Ajayi, sunce a halin yanzu garin ya zama abin tsoro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel